APC ta yi zargin ana yunƙurin daƙile tattara sakamakon zaɓe a Adamawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC ta zargi gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, da yunƙurin kawo cikas ga tattara sakamakon zaɓe.

Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamna daga ƙananan hukumomin har zuwa tsakar rana.

Farfesa Mohammed Mele, jami’in tattara bayanai na jihar da Yakubu Ari, kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, ne suka sanar da hakan a ranar Litinin bayan tattara sakamako daga ƙananan hukumomi 20 cikin 21.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na murɗe muradin al’ummar jihar a zaɓen gwamnan jihar.

Morka, wanda ya yi ikirarin cewa sakamakon zaɓen ya nuna gagarumar nasara ga ’yar takararta, A’isha Binani, ya bayyana kwarin gwiwar cewa alƙalan zaɓen da hukumomin tabbatar da doka za su tsaya tsayin daka tare da tabbatar da an kammala aikin zaɓen kamar yadda doka ta tanada.