Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar da takwaransa na LP Mista Peter Obi, na tattaunawa da Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) don komawa cikinta.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ne ya bayyana haka a shirin Sunday Politics na Channels Teleɓision. Wannan bayani na Adebayo ya biyo bayan sauya sheƙar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa SDP.
Adebayo ya ce, “Mutane suna shiga jam’iyyarmu, kuma muna maraba da su. Kuna gani yadda nake ƙoƙari wurin karɓar su. Kaɗan daga cikin matsalolin da muke da su da wasu daga cikinsu shi ne gyara ɗabi’a, musamman idan mutum bai saba da yanayi inda ake mutunta doka ba.
“El-Rufai, Atiku Abubakar, har da tsohon Gwamna Peter Obi—duk suna zuwa. Mutane da dama suna zuwa, kuma za mu marabce su. Ko da yake, har sai mutum ya shigo da kansa za mu tabbatar. Amma mutane sun faɗa min, har ma sakataren kuɗi na jam’iyyar ya shaida min suna tattaunawa. Don haka za mu marabce su.”
Adebayo ya ja kunnen masu shigowa jam’iyyar cewa kada su rikita jam’iyyar kamar “gidan Babel,” sai dai su mutunta dokokin jam’iyyar, su kuma ba da dama ta gaskiya ga ɗan takara ɗaya ya fito ba tare da rikici ko maguɗi ba, kamar yadda aka yi a taron gangamin jam’iyyar a 2022 wanda bai jawo gardama ko ƙara ba.
“In har za su rungumi ɗabi’ar mu a SDP, su kuma samar da wata sahihiyar madogara ga ‘yan Nijeriya, to lalle za mu doke jam’iyyar APC, mu kuma mayar da Shugaba Tinubu Legas ko inda ya zaɓa a Nijeriya.”
