Atiku ya lashe Sakkwato

*Mutum 254,902 ba su samu damar jefa ƙuri’a ba – INEC

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, yayi nasarar doke abokan fafatawarsa a Sokoto.

Atiku ya samu nasarar ne da ƙuri’u 288,679 wanda hakan ya ba shi damar doke babban abokin karawarsa na APC, Bola Ahmed Tinubu da ya samu ƙuri’u dubu 285,444.

Tunda farko, Tinubu ne ke kan gaba, amma daga bisani lamarin ya bayan isowar sakamakon ƙaramar hukumar Tambuwal da ya ba wa Atiku nasarar da tazarar ƙuri’u 3,235.

Peter Obi na Labour party ne ya zama n 3 a jihar da ƙuri’u 6,568 sai kuma Sanata Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da ya samu ƙuri’u 1,300.

Baturen zaben jihar Sokoto Farfesa Muhammadu Kabir ya bayyana cewa bisa samun hayaniya da wasu matsaloli a rumfuna 471 hukumar ta soke zaɓen da aka gudanar a waɗannan run’mfunan, abin da ya shafi ƙuri’un masu zaɓe a ƙalla 254,902.

Sai dai jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen, wakilin PDP a wajen tattara sakamakon zaɓen, Yusuf Suleiman ya buƙaci hukumar zaɓen data duba yuwar sake gudanar da wasu zaɓuɓɓukan a rumfunan da lamarin ya shafa.

“Sakamakon da aka ayyana ba iyakacin manufar al’ummar Sokoto kaɗai ba ne, musamman ma dai na mutum 300,000 da aka hana wa damar zaɓe saboda wasu ‘yan matsaloli inji shi”.

Sai dai a nasa ɓangaren wakilin jam’iyyar APC kana ministan kula da lamurran ‘yan sanda na ƙasa, Muhammadu Maigari Dingyaɗi, ya ce a irin wannan marar akwai buƙatar barin hukumar zaɓe ta INEC ta yi aikin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *