Atiku ya nemi samun masalaha tsakanin Ɗangote da NUPRC kan ɗanyen mai

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira da a samu maslaha daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya a kan ka-ce-na-ce tsakanin matatar Dangote da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya a kan batun samar da ɗanyen mai ga matatar.

A wasu jerin rubuce-rubucen da ya yi a shafin sa na ɗ a ranar Asabar, Atiku ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da nasarar aikin matatar man mai ƙarfin fotar da gangan 650,000 a kullum.

“Da wannan fahimtar, na yi taka-tsan-tsan wajen yin la’akari da duk wani yunƙuri na ganganci na kawo cikas ga ci gaban matatar Dangote, wani muhimmin aiki na kamfanoni masu zaman kansu da aka tanadi don biyan buƙatunmu na makamashi da kuɗin waje.

“Tare da ‘yan ƙasa da dama na fatan alheri, ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su ɗauki tsattsauran mataki don tabbatar da cewa sojojin ciki da na waje ba sa haɗa kai don hana mu cin gajiyar alfanun da aka yi mana alkawari ta hanyar wannan yunƙuri na kawo sauyi,” inji shi.

Rikicin ɗanyen mai da ya dabaibaye matatar mai na Dangote ya ɗauki sabon salo a ranar Juma’a, bayan da ƙungiyar Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gaza aiwatar da aikin ɗanyen mai a cikin gida yadda ya kamata.

Da take mayar da martani, NUPRC ta ce ta taimaka wajen samar da sama da ganga miliyan 29 na ɗanyen mai ga Dangote daga watan Janairu zuwa Yuni 2024.

By ukarofi