Atiku ya yi tir da kalaman gwamnatin Tinubu kan shirin Amurka na ƙaƙaba wa ƙasashe haraji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi aiki da abin da take da’awa ta hanyar fifita muradan Nijeriya ba nuna son zuciyarsu ba.

Ya kuma buƙaci gwamnatin da ta samar da haɗin kai da ɗinke ɓaraka da kaucewa yin kalamai marasa daɗi kan sauran ƙasashe da wasu ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa.

Atiku ya bayyana hakan ne a yayin da yake yi wa mai magana da yawun shugaban ƙasa, Sunday Dare, martani ta dandalin sada zumunta ta ɗ a ranar Asabar.

A ɗaya daga cikin rubuce-rubucen da ya yi, Mista Dare ya buƙaci sauran ƙasashe da su ɗaura ɗamarar fuskantar ƙarin harajin da gwamnatin sabon shugaban Amurka, Donald Trump take shirin yi ga ƙasashe.

Sannan a rubutunsa na biyu, mai magana da yawun shugaban ƙasar, ya yi wa shuwagabannin jam’iyyu siyasa a Nijeriya shaguɓe kan ƙoƙarin da suke yi na ƙarfafa dimokraɗiyya da samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya.

Sai dai a cikin jawabin da mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai ya yi, Paul Ibe, a ranar Lahadi, ya ce, Atiku ya yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu kan ta riƙa aiki da abin da take faɗa a baki.

Tinubu na cigaba da amfani da salon ƙwamushe wanda ke nuna cewa ba shi da niyyar ƙarfafa dimokraɗiyya a cewar Atiku Abubakar.

A yammacin ranar Asabar, 2 ga watan Fabarairu, mai taimaki na musamman kan yaɗa labarai ga shugaba Tinubu, mista Sunday Dare ya yi wasu rubuce-rubuce biyu a shafinsa na ɗ.

Rubutu na farko, ya buƙaci ƙasashe da su ɗauka ɗamarar fuskantar sabbin matakan haraji da shugaban ƙasar Amurka, Trump, zai ƙaƙaba wa ƙasashen duniya a shirinsa na ‘Sanya Muradan Amuka Farko’, sai kuma rubutu na biyu wanda a cikinsa, Dare, ya yi ƙoƙarin yi wa shugabannin jam’iyyun siyasa shaguɓe kan ƙoƙarin da suka na inganta dimokraɗiyya da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya.

Rubutunsa na biyu, ya so ya ci wa shugabannin siyasa fuska ne ta hanyar nuna rashin cancantarsu duk kuwa ƙoƙarin da suke yi shi ne na lalubo hanyar da ta dace domin ɗora Nijeriya a kai. Sai dai kalaman Dare, sun nuna irin yadda gwamnatin shugaba Tinubu ke ƙoƙarin gudanar da zaɓe mai zuwa a Nijeriya, wato, ‘a mutu ko ai rai’ ko kuma daɗa zafafa salon gwamnatinsa na ‘ƙwamushe’.

Don haka, wajibi ne mu gaya wa gwamnatin Tinubu cewa, taron da aka yi na shugabannin siyasa a makon da ya gabata, taro ne da manufarsa ita ce bunƙasa tsarin dimokraɗiyya na gari, domin tabbatar da ana gudanar da sahihin zaɓe da tabbatar da dimokraɗiyya a matsayin hanyar samar da cigaba da adalci a Nijeriya.

Don haka, muka cika da mamakin yadda gwamnatin Tinubu ta ayyana wannan taro da zama ‘maƙarƙashiya’.

Idan har gwamnatin Tinubu za ta riƙa amfani da kalamai da ake amfani da su a jahiliyya kan masu ‘yan jam’iyyar adawa, abu ne da bai kamata ba ko tauye ‘yancinmu da cin fuskar dimokraɗiyyar da muka samu da wuyar gaske.

ɗaya rubutun kuwa, Dare, ya ayyana yunƙurin shirin gwamnatin Trump – ‘Sanya Muradan Amurka Farko – da “salon yaƙin haraji”.

Da farko, muna All-wadai da kalaman mai magana yawun shugaba Tinubu, saboda wannan abu ne da ya shafi alaƙar Nijeriya da Amurka da sauran ƙasashen duniya da sauran hukumomin kasuwanci na duniya.

Kuma ban da wannan, kalamansa na cin karo da kalaman shugaba Tinubu na ɗabbaƙa gaskiya a cikin mulkinsa. Don haka, muna kiran gwamnatin Tinubu da ta riƙa amfani da abin da take faɗa a maimakon son zuciya.

Nijeriya ƙasa ce da a yanzu ke fuskantar ƙalubale daban-daban kamar na rarrabuwar kai na ƙabilanci da addini tun bayan hawan gwamnatin Nijeriya.

Wannan ita ce gwamnati ta farko a tarihi da ta fara fito bambancin ta hanyar ɓullo da rukunin wutar lantarki na “ rukunin A ‘Band A’ da rukuni na ‘Band C’ a tsarin zamantakewar Nijeriya da samun kayan abin more rayuwa.

Don haka, muna kira ga gwamnatin Tinubu da ta haɗa kai wajen ɗinke ɓarakar da ke Nijeriya da kauce wa yin kalamai marasa kan gado kan wasu ƙasashen duniya da kuma ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa.

By ukarofi