‘Yan sanda a Kebbi sun gano wani gida maƙare da baƙin-haure 165 a Birnin Kebbi 

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta hannanta waɗansu ‘yan ƙasashen waje su kimanin ɗari da sittin da biyar ga hukumar shige da fice da ke jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana haka ne lokacin da take gabatar da mutanen ga manema labarai a shalkwatar ‘yan sanda da ke Gwadangwaji Birnin Kebbi ranar Talatar da ta gabata.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa kama waɗannan mutanen ya biyo bayan samun bayanan sirri da ta yi inda ita kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta tura jami’an ta na ‘yan sandan ciki don binciko haƙiƙannin gaskiyar lamarin, wanda sanadiyyar haka hukumar ta gano mutane sama da ɗari biyu suna zaune a wani gida mai ɗakuna uku a unguwar Kuwait da ke cikin garin Birnin Kebbi.

Rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kama mutane ɗari da sittin da biyar da bincike ya tabbatar da dukkaninsu sun fito ne daga ƙasashen mulkin mallakar Faransa ne inda talatin da biyar daga cikinsu sun fito ne daga ƙasar Burkina Faso, goma sha ɗaya daga ƙasar Benin,  biyar daga Jamhuriyar Nijar, huɗu daga ƙasar Mali, sai ɗari da goma daga Iɓory Coast.

Binciken da rundunar ‘yan sandan ta gudanar ya nuna waɗannan mutanen suna zaune ne a ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba suna gudanar da harkokin kasuwancin saka jari na ko a faɗi ko a ci riba yayin da waɗansu kuma ke neman aikin yi kamar yadda binciken ya nuna.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi Bello M Sani ya bayyana cewa bayan kammala binciken kuma an hannanta dukkaninsu ga hukumar shige da fice da ke garin Birnin Kebbi don ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi