Majalisar Dattawa ta canja jagororin wasu kwamitoci, ta sake naɗa sabbin shugabanni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana jin daɗinsa da yadda aka kammala zaman kare kasafin kuɗi da aka kammala, inda ya yaba wa ‘yan majalisar bisa jajircewarsu wajen tantance kasafin kuɗin shekarar 2025 domin tabbatar da tsarin kuɗi na shekarar ya inganta.

Shugaban majalisar dattawan ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar bayan hutun makonni biyu.

A halin da ake ciki dai, bayan amincewar da Shugaba Bola Tinubu ya yi kan ƙudirin kafa kwamitocin raya ƙasa a yankuna daban-daban na ƙasar nan, Majalisar Dattawa ta gudanar da wani ƙaramin sauyi, inda ta naɗa shugabanni da mataimakansu da za su riƙa kula da waɗannan kwamitocin.

A cewar Akpabio, Sanata Babangida Hussaini da Sanata Muntari ɗandutse za su yi aiki a matsayin shugaba da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma.

Hakazalika an naɗa Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Kenneth Eze a matsayin shugaba da mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan Hukumar Raya Kudu maso Gabas, yayin da Sanata Titus Zam da Sanata Isa Jibrin za su jagoranci kwamitin majalisar dattawa mai kula da Harkokin Ci Gaban Arewa ta Tsakiya.

A wani lamari makamancin haka, majalisar dattawa ta yi wa shugabannin wasu kwamitoci garambawul. An cire Sanata Abdul Ningi daga kwamitin kula da yawan jama’a ya zama shugaban kwamitin majalisar dattawa kan FERMA.

Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, wadda a baya ita ce mai kula da kwamitin kula da abubuwan cikin gida, a yanzu ita ce shugabar kwamitin kula da ‘yan ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Sauran sabbin shugabannin kwamitocin da aka naɗa sun haɗa da Sanata Garba Maidoki, wanda a yanzu yake shugabantar kwamitin raya wasanni na majalisar dattawa, da kuma Sanata Joel Thomas wanda shi ne sabon shugaban kwamitin majalisar dattawa kan abubuwan cikin gida.

An mayar da Sanata Victor Umeh daga kwamitin ‘yan ƙasashen waje kuma yanzu zai zama shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan al’umma da NIMC.

A halin da ake ciki, Majalisar ta yi ta’aziyya ga shugaban majalisar bisa rasuwar tsohon mataimakin mai rinjaye, Hon. Oriyomi Onanuga, ranar 15 ga Janairu.

Akpabio ya jagoranci sauran ‘yan majalisar yin shiru na minti ɗaya don karrama ta kafin a ɗage zaman.

By ukarofi