Kasuwar Mile-12 a Legas ta ƙaddamar da na’urar wanke kiret ɗin tumatiri

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Alhamis ɗin makon jiya, kasuwar Mile-12 da ke cikin birnin Legas a ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam ta gudanar da taron ƙaddamar da injinan wanke kiret da ake amfani da shi wajen ɗaukar tumatiri daga a rewacin Nijeriya zuwa cikin garin Legas.

Taron wanda ya haɗa da shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam da shugaban vangaren tumatiri Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano da shugaban ƙungiyar dattawan kasuwar Alhaji Isa Mohammed mai Shinkafa wanda ya samu wakilcin ɗaya daga cikin dattawan kasuwar Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki.

Sauran sun haɗa da sakataren ƙungiyar dattawan kasuwar Alhaji Abdulwahab tsoho Babangida tare da shuwagabannin vangarorin kasuwar da sauran masu ruwa da tsaki bisa kan harkokin kasuwancin gwari a Legas.

Taron dai ya gudana ne a harabar ofishin kasuwar dake babbar kasuwar ƙasa da ƙasa ta Mile-12.

Da yake gudanar da jawabinsa a matsayinsa na shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam ya bayyana ƙudurinsu na gudanar taro inda ya ce sun gabatar da taron ne domin ƙaddamar da injinan tsaftace kiret ɗin roba wanda suke amfani da shi wajen ɗaukar tumatiri daga arewacin Nijeriya zuwa Legas tare da nunawa duniya irin na’urorin da suka samarwa kasuwar domin wanke kiret kafin zuba masa tumatiri zuwa Legas domin kare lafiyar al’umma.

Ya ce a wancan lokacin suna amfani da kwanduna ne a wajen safarar tumatirin zuwa kasuwar Mile-12 amma yanzu an samu cigaba, hakan ta sanya suke amfani da kiret ɗin roba a wajen ɗauko tumatiri zuwa kasuwar saboda yana rage masu faruwar lalacewar tumatirin a hanyarsa ta shigowa Legas.

Ya ce kuma sun lura saboda cinkoson jama’a wurin da ake ajiye kiret ɗin kafin kwaso shi zuwa arewacin Nijeriya mutane suna fitsari a gefen wurin waɗansu ma su yi kaki su tofa a kai wanda a cewarsa idan aka yi dace da waɗansu suna ɗauke da cutar tarin fuka al’umma da yawa suna iya kamuwa da cutar.

Shi ma a nasa tsokacin Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, wanda shine shugaban vangaren tumatiri a kasuwar bayan ya kammala nuna farin cikin sa dangane da wannan al’amari ya ce za su cigaba da kawo tsare-tsaren da za su kawo cigaban kasuwancin tumatiri da sauran kayan miya a Legas.

Sauran jawaban da suka gudana a wajen taron waɗan da suka fito daga bakunan dattawa Alhaji Habu Faki Garkuwan Faki da sakataren ƙungiyar dattawan kasuwar Alhaji Abdulwahab Tsoho Babangida da sauran al’ummar da suka samu yin tsokaci a wajen taron dukkan jawabansu sun karkata ne wajen sanya alheri dangane da wannan al’amari.

By ukarofi