Editor

9513 Posts
Makamashi: Kora ta kai bango

Makamashi: Kora ta kai bango

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Ga masu Shugabanni masu hangen nesa a kasarsu, kamar yadda Kamus na Hausa ya yi tarihin kalmar Turanci ‘Focus’ da ya ‘mai da hankali kan” wani abu, da sai mu ce sambarka da fadi-tashin da Majalasar Dinkin Duniya ta kwashe sama da shekaru 30 kan ‘sauyin yanayi’, wanda ya jefa wasu daga cikin kasashen duniya ka kanakayi bisa gonaki, a wasu guraren kuma a ka sami kamfar ruwa, wanda ya kawo qarancin abinci ga bil adama da dabbobi da tsintsaye. Sauyin yanayi shi yake haifar da kadawar iska daga teku zuwa doran kasa, inda ta…
Read More
Gobe Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabin sabuwar shekara

Gobe Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabin sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH Gobe Litinin, 1 ga Janairu, ake sa ran Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa 'yan kasa jabi albarkacin shiga sabuwar shekarar 2024. Kakakin Shugaba Kasa, Ajuri Ngelale, ya bayyana a sanarwar da ya fitar yau Lahadi cewa, da karfe 7:00 na safe ne ake sa ran Shugaban ya gabatar da jawabin nasa. "Don haka ake kira ga tashoshin talabijin da na rediyo da sauran kafafen yada labarai da su jona da tashoshin talabijin da rediyo na gwamnati don yada jawabin," in ji shi. Wannan shi ne karon farko da Tinubun zai yi wa 'yan kasa…
Read More
An sha jarabtar tashin hankali da rashin zaman lafiya a shekarar 2023 – MƊD

An sha jarabtar tashin hankali da rashin zaman lafiya a shekarar 2023 – MƊD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce shekarar 2023 ita ce shekarar da ta jawo wahala da tashin hankali a fadin kasashe. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya bayyana hakan a wani sako na bidiyo da aka fitar a jajibirin shekarar 2024. A cewarsa “bil'adama na cikin zafi. Duniyarmu tana cikin babban matsala. 2023 ita ce shekarar da ta fi zafi a tarihi. mutane na mutuwa ta hanyar karuwar talauci da yunwa. Yaƙe-yaƙe da tashin hankali suna ƙaruwa da yawa Kuma amana ta yi karanci. “Amma nuna wa juna yatsa da zuwa yaƙe-yaƙe ba za su kawo mafita ba”.…
Read More
Ƙaruwar bashin da ake bin Nijeriya abin damuwa ne

Ƙaruwar bashin da ake bin Nijeriya abin damuwa ne

Ga duk mai bibiyar kafafen yada labarai zai ji cewa, Nijeriya ta kara shiga tsaka mai wuya kan yawan bashin da kasar ke kara ciwo wa kanta. Yawan bashin da gwamnatin Nijeriya ta ciyo ya karu zuwa Naira tiriliyan 42, a cewar Ofishin Kula Basuka na Kasa (DMO). Ofishin ya cewa a cikin wata uku, daga Maris zuwa Yuni na 2023, Nijeriya ta ciyo karin bashin Dala biliyan uku, wanda ya sa abin da ake bin ta karuwa zuwa Dala biliyan 103.31 daga Dala biliyan 100. Hakan na nufin idan aka raba wa ’yan Nijeriya mutum miliyan 200 bashin, kowannensu…
Read More
Kisan Filato: Shettima ya ziyarci al’ummar Bokos, ya ba da tabbacin yin adalci ga waɗanda abin ya shafa

Kisan Filato: Shettima ya ziyarci al’ummar Bokos, ya ba da tabbacin yin adalci ga waɗanda abin ya shafa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai wadanda hare-haren wuce gona da iri da aka kai kan al’ummar kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos na Jihar Filato su samu adalci kuma mazauna yankin sun tsira. Mataimakin Shugaban Kasar, Kashim Shettima, ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci al’ummomin da rikicin ya rutsa da su a jihar Filato domin jajantawa jama’a da gwamnatin jihar kan kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos. Da yake shan alwashin cewa dole ne a kawo karshen kashe-kashen…
Read More
Mun ba da lasisi ga kamfanonin tsaro masu zaman kansu 93 a cikin 2023 – NSCDC

Mun ba da lasisi ga kamfanonin tsaro masu zaman kansu 93 a cikin 2023 – NSCDC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya, NSCDC, ta ce ta bayar da lasisin gudanar da aiki ga kamfanoni masu zaman kansu 93, PGCs, a shekarar 2023 domin karfafa tsaron kasa. Kwamandan hukumar ta NSCDC Janar Ahmed Audi ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai a hedikwatar hukumar ranar Laraba a Abuja. Audi ya ce daga cikin jimillar PGC 1,412 da hukumar ta yi wa rajista, 92 an rufe su a fadin kasar nan saboda wasu laifukan da suka sava wa aiki amma 24 daga cikin PGC da suka kasa cika a shekarar…
Read More
Waiwayen muhimman abubuwan da suka faru a 2023

Waiwayen muhimman abubuwan da suka faru a 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shekara ta 2023 ta zo qarshe, kuma daya daga cikin abubuwan da za a iya cewa a kanta shi ne, shekarar cike ta ke da al’amura masu kyau da munana da suka afku. Batutuwa kamar tsadar rayuwa, rikice-rikicen ’yan Boko Haram da ISWAP, ’yan bindiga masu satar mutane da kuma rikata-rikitar siyasa sun mamaye yawancin kwanakin shekarar. Bisa ga dukkan alamu, shekarar 2023 ta zama abar ban tsoro. Za a tuna ta a matsayin shekarar kunci. Hatta Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi ishara da hakan a sakonsa na Kirsimeti, inda ya ce, shekara ce ta…
Read More
MDD ta yi maganar rayuka 190 da aka kashe a Filato

MDD ta yi maganar rayuka 190 da aka kashe a Filato

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna bacin ran ta game da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan jihar Filato a karshen shekarar nan. Shugaban kula da hakkin bil adama a majalisar Dinkin Duniya Volker Turk, ya sanar da haka ne a wani jawabi da ya fitar a yammacin ranar Alhamis. Mista Volker Turk ya nuna akwai matukar bukatar a yi gaggawar kawo karshen wannan kashe-kashen. A cewarsa “Ina mai matukar damuwa da jeringiyar hare-haren ‘yan bindiga a kauyuka da-dama da ke jihar Filato." "Ina kira ga hukumomin Najeriya su binciki wannan lamari da wuri kuma da kyau, bisa…
Read More
2024: Majalisar Tarayya ta amince da kasafin N28.7tn

2024: Majalisar Tarayya ta amince da kasafin N28.7tn

Daga BASHIR ISAH A zaman hadakar da suka yi a ranar Asabar, Majalisar Dattawa ta amince da N28,777,404,073,861 s matdayin kasafin 2024. Dai dai, a yayin zaman nata, Majalisar ta kara kasafin da Naira tiriliyan 1.2 kan Naira tiriyan 27.5 da Shugaban Kasa ya gabatar wa majalisar a ranar 29 ga Nuwamban 2023. Majalisar ta kara kasafin da tiriliyan 1.2 ta kuma kara farashin canjin Dala da yawan danyen mai da za a rika hakowa. Haka nan, ta amince da tiriliyan N28.7 a matsayin kasafin 2024, bayan nazarin rahoton kwamitinta na kasafin kudi. Kazalika Majalisar ta daga farashin canji Dala…
Read More
Bayan Sasancin Gwamnan Zamfara, an buɗe Masallacin Juma’ar da ya shekara bakwai a rufe

Bayan Sasancin Gwamnan Zamfara, an buɗe Masallacin Juma’ar da ya shekara bakwai a rufe

Gwamna Dauda Lawal ya sasanta rikicin shekara bakwai (7) da ya kai ga rufe ɗaya daga cikin manyan masallatan Juma’a na garin Moriki daje ƙaramar hukumar Zurmi. An rufe masallacin Juma'ar na Moriki sama da shekaru bakwai (7) sakamakon taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ɓangarori biyu na al'ummar yankin. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau, ya ce ɗaukar matakin ya zama dole domin magance matsalar rashin haɗin kan jama’a. A cewarsa, gwamnan ya lura da muhimmiyar rawar da haɗin kai ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kuma samar…
Read More