Editor

9513 Posts
Akwai waƙoƙin da bai dace a ce Hausawa ne ke yin su ba – Tijjani Gandu

Akwai waƙoƙin da bai dace a ce Hausawa ne ke yin su ba – Tijjani Gandu

DAGA MUKHTAR YAKUBU A watan Agustan ne Gwamnatin Jihar Kano ta nada fitaccen mawaki Tijjani Hussaini Gandu a matsayin Babban Mataimakin na Musamman ga Gwamnan Kano kan harkar wallafa, mukamin da shi ne na farko da aka tava yi a tsarin tafiyar da Gwamnatin Kano. Wakilinmu ya tattauna da Tijjani Gandu domin jin matsayin ofishin nasa da kuma ayyukan da zai rinka gudanarwa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance. MANHAJA Tijjani Gandu, kana daya daga cikin fitattun mawaka a fagen siyasa a kasar nan kuma ka samu kanka a cikin wadanda aka nada a…
Read More
Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (2)

Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (2)

Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mun kwararo bayani kan yadda lokacin sanyi ke tasiri ga lalacewar fata da kuma gashin kai, sannan mun fara kawo wasu hanyoyin da za a bi don kaucewa lalacewar fata a lokacin. A wannan satin ma za mu ci gaba da darasin namu ne da karin wasu hanyoyi na kaucewa matsalar fata a lokacin hunturu. Yawaita shan ruwa: a lokacin sanyi, bukatuwar mu da ruwa kan ragu sosai ta yadda za ka iya daukar tsayin lokaci ba tare da ka ji bukatar ruwa ba, don haka muke kauce wa shan su, sai…
Read More
Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin 2024

Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin 2024

Daga BASHIR ISAH    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin 2024 na Naira tirilyan 28.7 wanda hakan ya sanya  kasafin zama doka. A ranar Litinin da ta gabata Tinubu ya sanya wa kasafin hannu da misalin karfe 2:00 na rana a ofishinsa, inda aka shirya kwarya-kwaryar biki wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnatinsa. Mahalarta bikin sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Shugaban Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas; Ministan Kudi, Mr Wale Edun. Sauran sun hada da Ministan Kasafi da tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Bagudu; Mai bai wa Shugaban Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA),…
Read More
KASSOSA ta karrama Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmuwa da yake bayarwa

KASSOSA ta karrama Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmuwa da yake bayarwa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Honarabul Mustapha Bala Dawaki ya bayyana karramawar da kungiyar tsaffin dalibai na Makarantun Kimiyya ta Kasa (KASSOSA) ta yi masa a yayin taronta na shekara da aka gudanar a jami'ar Bayero  rantsar da sabbin shugabaninta da cewa abin godewa ne ga Allah kuma sun yi duba ne da irin abubuwa da akai musu na alkhairi wajen kawo cigaba a makarantunsu na kimiyya. Tsohon dan majalisar mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa ya ce irin abubuwa na gine-gine da hanyoyi sa wutar lantarki da ruwa da bunkasa harkar iliminsu ita tasa suka ga cancantar karramashi a…
Read More
ACF za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta zaman lafiya – Ƙungiyar Matasan Arewa

ACF za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta zaman lafiya – Ƙungiyar Matasan Arewa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Kungiyar Tuntuva ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa kungiyar ta shirya tsaf domin samar da zaman lafiya, hadin kai da samar da wadata a fadin Arewacin Nijeriya baki daya bisa ingantaccen tsari. Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin matasan Arewa (JACOM), sun yi amanna da kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) domin ganin an samu sauyi tare da sauya akalar shugabancin kungiyar ta fannin zamantakewa da al’adun Arewacin Nijeriya. Kungiyar Matasan Arewa, a wata sanarwa da Murtala Abubakar, shugaban JACOM da Israel Musa, Sakatarenta suka…
Read More
Don amfanin ƙasa na ɗauki tsauraran matakai – Tinubu

Don amfanin ƙasa na ɗauki tsauraran matakai – Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shuagaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, tsauraran matakan da ya dauka tun bayan da ya karbi ragamar mulkin kasa, ya yi hakan ne domin ceto Nijeriya daga fadawa halin ha’ula’i. Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin sabuwar shekarar da ya yi wa ‘yan kasa da safiyar ranar Litinin, wanda aka yada kai tsaye a kafafen yada labarai. A cewarsa, “Dukkan abin da na yi a ofis, duk wani mataki da na dauka, duk wata tafiya da na yi zuwa wajen kasa tun bayan da na shiga ofis ran 29 ga Mayun 2023, na yi hakan…
Read More
Ƙungiyar KADDA ta gudanar da taron shekara

Ƙungiyar KADDA ta gudanar da taron shekara

Daga WAKILINMU Cikin 'yan kwanakin nan ne kungiyar cigaban cikin garin Kaduna, Doka, Wato KADDA ta gudanar da taron ta na shekara-shekara, inda Shugaban kungiyar, Honorabul Sani Rabi'u Bako ya bayyana nasarorin da su ke samu da cewa wani al'amari ne daga Allah madaukakin Sarki. Honarabul Bako ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron kungiyar na bana, inda aka gabatar da muhimman jawabai da kuma bayar da satifiket da lambobin karramawa na shekarar 2023. Sani Rabi'u Bako, ya ci gaba da cewa duk da wannan Kungiyar ba ta siyasa ko…
Read More
2024: Gwamna Lawal ya rattaba hannu kan kasafin  N426bn

2024: Gwamna Lawal ya rattaba hannu kan kasafin  N426bn

Daga BASHIR ISAH A ranar Asabar da ta gabata Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannun kan kasafin shekarar 2024 na Naira biliyan 426. Kasafin wanda aka yi wa take da “Kasafin Ceto”, ya samu amincewar Majalisar Dokokin Jihar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda washegari Gwamnan ya rattaba hannu ya zama doka. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a sanarwa da ya fitar cewa, daga cikin N426,563,671,000.00 da aka amince da shi a matsayin kasafin 2024, an ware wa ayyukan yau da kullum N118,358,079,515.00, yayin da aka ware wa muhimman ayyuka N308,205,591,485.00.…
Read More
Emefiele, daga kukan targaɗe an koma karaya

Emefiele, daga kukan targaɗe an koma karaya

Tare da NASIRU ADAMU EL-HAKAYA Hakika duk mai bin bayanan da su ka biyo bayan cika ka'idar da ta sa tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Godwin Emefiele ya samu ficewa daga gidan yarin Kuje zai iya fahimtar tafiyar sa gida tamkar hutun jaki ne da kaya a ka. Akasarin wadanda su ka samu beli na samun sararawa don in ma akwai dace shikenan sun huta da zaman gidan yari. A wasu shari'un ma za ka taras wani har rai ya yi halin sa ba a gama sauraron karar da a ka shigar da shi ba.  In ka debe irin…
Read More
Za a ƙara farashin jaridu a watan Janairun 2024 – NPAN

Za a ƙara farashin jaridu a watan Janairun 2024 – NPAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Masu Kamfanonin Wallafa Jaridu ta Nijeriya, wato 'The Newspaper Proprietors’ ta bayyana kara kudin jaridu a sabuwar shekara. Association of Nigeria (NPAN)' ta bayyana cewa daga ranar 2 ga watan Janairun 2024 sabon farashin jaridu zai fara aiki a duk fadin aasar nan. Babban Sakatare na Kungiyar ta NPAN, Feyi Smith ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a Abuja cikiin makon da ya gabata. Mr Feyi ya ce, "Kungiyar mu da dauki wannan tsattsauran mataki ne bisa nazarin da ta yi na matsin tattalin arzikin da mambobin mu…
Read More