Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin 2024 na Naira tirilyan 28.7 wanda hakan ya sanya kasafin zama doka.
A ranar Litinin da ta gabata Tinubu ya sanya wa kasafin hannu da misalin karfe 2:00 na rana a ofishinsa, inda aka shirya kwarya-kwaryar biki wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnatinsa.
Mahalarta bikin sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Shugaban Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas; Ministan Kudi, Mr Wale Edun.
Sauran sun hada da Ministan Kasafi da tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Bagudu; Mai bai wa Shugaban Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu; Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje da dai sauransu.
A ranar Juma’ar da ta gabata ‘yan majalisar tarayya suka yi zama ta hadaka inda a nan suka amince da kasafin wanda hakan ya bai Tinubu damar sanya hannu ya zama doka.