KASSOSA ta karrama Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmuwa da yake bayarwa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Honarabul Mustapha Bala Dawaki ya bayyana karramawar da kungiyar tsaffin dalibai na Makarantun Kimiyya ta Kasa (KASSOSA) ta yi masa a yayin taronta na shekara da aka gudanar a jami’ar Bayero  rantsar da sabbin shugabaninta da cewa abin godewa ne ga Allah kuma sun yi duba ne da irin abubuwa da akai musu na alkhairi wajen kawo cigaba a makarantunsu na kimiyya.

Tsohon dan majalisar mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa ya ce irin abubuwa na gine-gine da hanyoyi sa wutar lantarki da ruwa da bunkasa harkar iliminsu ita tasa suka ga cancantar karramashi a matsayinsu na daya daga tsofaffin dalibai ‘yan kungiyar.

Mustapha Bala Dawaki ya ce, yana godiya kwarai da gaske da har suka ga ya cancanta su bada wannan karramawa a gareshi kuma da yardar Allah za su cigaba da taimawa makarantu da duk harka da ta shafi cigaban karamar hukumar Dawakin Kudu da Warawa da jihar Kano da kasa bakidaya in Allah ya bada dama.

Ya yi lira ga yan kungiyar akan su cigaba da bibiyar mutane masu hali ’yan boko da masu mukaman Gwamnati musamman da yake a dalilin makarantun na kimiyya da aka samu akwai manyan mutane a mukamai daban-daban Wanda kawai basu dashi shi ne na shugaban kasa.

Mustaph Bala Dawaki ya ce, an sami wanda ya yi gwamna, mataimakin gwamna da Sanata, dan majalisar tarayya da na jiha da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da sarakuna hakimai daga wadanda makarantar ta yaye don haka a cigaba da bibiyar irin wadannan mutane kowa akwai irin gudunmuwa da zai iya bayarwa.

By Editor