Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (2)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, mun kwararo bayani kan yadda lokacin sanyi ke tasiri ga lalacewar fata da kuma gashin kai, sannan mun fara kawo wasu hanyoyin da za a bi don kaucewa lalacewar fata a lokacin.

A wannan satin ma za mu ci gaba da darasin namu ne da karin wasu hanyoyi na kaucewa matsalar fata a lokacin hunturu.

Yawaita shan ruwa: a lokacin sanyi, bukatuwar mu da ruwa kan ragu sosai ta yadda za ka iya daukar tsayin lokaci ba tare da ka ji bukatar ruwa ba, don haka muke kauce wa shan su, sai dai abinda ba mu sani ba shi ne, bincike ya tabbatar da cewa, fata na matuqar bukatar ruwa a lokacin sanyi, don hana ta yawan bushewa da kuma kara mata inganci, don haka rashin isasun ruwa a jiki na daya daga cikin ababen da ke taimako wurin bushewar fata a lokacin sanyi.

Gyaran jiki: Akwai gyaran jiki da mata ke yi musamman lokacin da za su iya aure, don qara wa jikinsu kyau, sai dai wasu daga cikinsu na hawa layin abubuwan da ke kawowa fata agaji a lokacin sanyi, kamar dilka da halawa.

Yana da kyau mata su sanya irin wannan gyaran jiki a layin ababen da suke yi a lokutan sanyi, don ganin fatarsu ba ta shiga mawuyacin hali ba.