Akwai waƙoƙin da bai dace a ce Hausawa ne ke yin su ba – Tijjani Gandu

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A watan Agustan ne Gwamnatin Jihar Kano ta nada fitaccen mawaki Tijjani Hussaini Gandu a matsayin Babban Mataimakin na Musamman ga Gwamnan Kano kan harkar wallafa, mukamin da shi ne na farko da aka tava yi a tsarin tafiyar da Gwamnatin Kano.

Wakilinmu ya tattauna da Tijjani Gandu domin jin matsayin ofishin nasa da kuma ayyukan da zai rinka gudanarwa. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA Tijjani Gandu, kana daya daga cikin fitattun mawaka a fagen siyasa a kasar nan kuma ka samu kanka a cikin wadanda aka nada a mulkin Gwamnatin Jihar Kano inda aka nada ka a matsayin babban mataimaki ga gwamnan Kano kan harkar wallafa, don haka muna son ka yi wa masu karatun mu karin bayani a game da wannan mukami.

TIJJANI GANDU: To Alhamdulillahi haka ne mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ba ni matsayi na babban mataimaki na musamman kan harkar mawallafa. Wannan shi ne mukamin da aka ba ni.

Idan aka ce wallafa tana da fadi, akwai wakokin baka da na rubutu da litattafai, jaridu da wakokin yabon Manzon Allah da dai sauran abubuwa na wallafa masu yawa.

Kai a wanne bangare mukamin ka ya tsaya?

In dai a Kano ka ke ka na harkar wallafa, to a karkashin ofishina ka ke, da ita wawa, da labarai na soyayya da hikayoyi da tatsuniyoyi, da duk wani abu da ya shafi wallafa, to ni wakilin su ne a wajen maigirma gwamna.

To ya ya tsarin gudanarwar ofishinka zai kasance ta hanayar aiki?

Na farko ilmintar da mawallafa musamman wadanda ba su yi suna ba a cikin harkar, kuma su ke so su yi suna, don a na samun da yawa ba su da ilimin abin, don haka muna son gwamnati ta yi mana gatan da za ta bada wata dama da kowanne mawallafi zai je ya yi karatu ko da a bangaren sa ne ta yadda zai samu shaidar ya yi karatu a fannin sana’ar sa, da kuma wasu abubuwa da za mu fito da su na tsaftacewa da gyarawa a kan wannan harkoki namu na wallafa.

Don idan ka duba idan na ce gyara akwai wakokin da bai gace a ce Hausawa ne suke ji ko suke wallafa wannan wakokin ba, to dole in dai muka samu dama irin wadannan abubuwan da a ke yi da ba su dace ba, za mu bada shawara ga masu yi su daina, idan kuma ba su daina ba, sai mu hada su da hukumar da za ta hukunta su, a kan wannan aikace-aikacen nasu na ba daidai ba.

A dunkule dai muna son mu kawo wa harkar ci gaba ne, yadda ko da bayan mun gama namu ko bayan ran mu abin zai dore na baya su ci gajiyar sa.

A yanzu an samu a wani yanayi yadda harkar wakokin siyasar da na soyayya da ma na yabon Manzon Allah kowanne vangare a na yin korafin shigar da abubuwan da ba su dace ba.

To kowanne bangare kamar yadda muka tsara za mu zauna da kowacce kungiya, kamar bangaren yabo suna da shugabanci, masu harkar Hip poh suna da shugabanci, idan ma ba su da shi za mu sa su yi duk za mu zauna da su, mu fada musu ga dama da muka samu, kuma su ba mu hadin kai domin a gudu tare a tsira tare.

A yanzu da yake lokaci ne na soshiyal midiya za ka ga wasu wakokin mutum ne shi kadai zai zauna a daki ya shirya ya fadi duk abin da ya ga dama na cin mutunci ya tura a soshiyal midiya. Wanne mataki za ku dauka a kan irin wadannan?

Duk dai maganar gyaran ce, kamar yadda na fada a baya, ko da ba ka cikin kungiya kai kadai a ware ka je ka yi waka ta rashin da’a ne, in dai a Kano ka ke, ko kuma kai dan Kano ne ka fita wani waje ka yi ka ke turowa, to muna da hanyar da za mu je mu same ka mu ja maka kunne, idan kuma ka ki ji, to sai mu hada ka da inda ya dace domin daukar mataki a kanka.

Ita harkar fasaha baiwa ce wadda da dama a yanzu ba masu baiwar ba ne, kawai dai a na yi mata taka haye saboda a na samun kudi. Ta yaya za ku magance kwararowar mutane cikin ta a irin wannan yanayin?

To akwai shirin da muke da shi na shirya taruka na karawa juna sani da kuma taron sanin makamar aiki da su kungoyoyin. To a wannan za mu jawo masana da suka san muhimmancin wallafa da baiwar don a sanar da mutane idan ka samu kanka a cikin masu wannan baiwar don ya zamana ka iya tafiyar da kanka, kada a yi ta zama barkatai kowa yana yin abin da ya ga dama ta yiwu Allah ya baiwa mutum dama bai sani ba. Don haka za mu nusar da mutane cewa idan Allah ya ba ka dama sai ka yi amfani da ita.

Hakar ku ta wakar siyasa a nan a ke ganin ya fi muni wajen cin mutunci da zage-zage da kalamai dai na zafafawa, ko wanne irin mataki za ku dauka?

To ita wakar siyasa ba ka raba ta da zambo, kuma shi zambo a wakar siyasa za a iya cewa halas ne. To amma cin mutunci bai zama halas ba. Don haka masu cin mutuncin mutane a wannan gwamnatin in Allah ya yarda ba za mu yarda da wannan ba, za mu dauki mataki a kan su.

Ko kuma za mu sa a dauki mataki a kan su matukar suka ci gaba da yin wannan cin mutuncin. Don haka abin da zan fada ga su mawallafa kowa ya yi kokari ya shiga kungiya idan bangaren yabo ka ke ka samu kungiyar yabo ka shiga, idan bangaren soyayya ka ke ko wakokin siyasa dole ya zama ka na cikin kungiya dai ta mawaka. Masu rubuce rubuce na san suna da kungiya, an fi samun katsalar a wajen mawaka, don haka duk wanda ba shi da kungiya sai ya yi kokari ya yi , domin idan aiki ya zo, ba wai da daidaikun mutane za a yi ba, za a yi ne ta karkashin kungiya, kuma za mu rinka bibiyar su don gwamnati ta san da zaman su, abin da ya kama na taimako gwamnati ta yi musu.

Ko akwai sabunta rajistar kungiyoyin mawallafa da ofishin ka zai yi a nan gaba?

E akwai wannan, don muna son mu sabunta rajista, da kuma yunkurin fadada kungiyar a kananan hukumomi 44 na Jihar Kano. Wannan Ina yin magana ne ga kungiyar mawaka, amma sauran kungiyoyi, ba mu ne muke da hurumin yin hakan ba, mu dai idan suka zo mana a kungiyance za mu karbe su, kuma abin da ya kama na gyara za mu yi musu.

To su kungiyoyin mawallafa za su zauna a inuwar kungiya daya ne kamar yadda a bangaren ‘yan fim suke da wannan tsarin?

E to ba mu zo da wannan ba, amma dai muna son mu zama a dunkule ka san a na yin wakilci, don haka duk wani mai harkar wallafa a yanzu ni ne wakilin sa a Gwamnatin Jihar Kano, ta karkashin ofishina za a rinka gudanar da wannan tsarin da ya shafi harkar wallafa.

Don ka ga idan ka dauke kungiyar marubuta littattafai da ta mawallafa wakoki a cikin mu dai in ban da kungiyar mu ta mawakan Kwankwasiyya ba na jin akwai wata kungiya ta mawaka ta kasa da take da rajista, saboda haka ta karkashin ofis dina ne wadannan ayyuka za su rinka fita. Don haka kowa ya mayar da hankali wajen neman ilimi, da kuma xaukar abubuwan da suke da muhimmanci.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode Sosai.