Editor

9513 Posts
A yanzu ana kallon marubuci kamar wanda bai san kansa ba – Ayusher Muhammad

A yanzu ana kallon marubuci kamar wanda bai san kansa ba – Ayusher Muhammad

"Kaso sittin bisa ɗari Ina wa rubutu kallon sha’awa ne" DAGA MUKHTAR YAKUBU Aisha Muhammad Salis, wadda aka fi sani da Ayusher Muhammad a harkar rubutun onlayin, ta na daga cikin fitattun marubutan soshiyal midiya da a yanzu ake yayin su. Haka kuma tana da basira da salon kirkirar labari da rubutawa. Don haka ne ma ta yi fice a cikin marubutan da ake ji da su a onlayin. Domin jin ko wacece Ayusher, wakilin Blueprint Manhaja a Kano, ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance. MANHAJA: Da farko dai za…
Read More
Hannutu Musawa ta buƙaci a tallafa wa jarumi Zack Orji kan jinyarsa

Hannutu Musawa ta buƙaci a tallafa wa jarumi Zack Orji kan jinyarsa

Daga BASHIR ISAH Ministar Kirkire-kire da Al’adu, Barista Hannatu Musawa, ta yi kira ga masu hali a Nijeriya da su dubi Allah su taimaka wa jarumin masa’antar Nollywood, Zack Orji, bisa jinyar da yake yi a halin yanzu. A ranar Litinin da ta gabata aka yi wa jarumin aiki na lalurar da yake fama da ita mai nasaba da kwakwalwa. Wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun hadimarta, Nneka Ikem Anibeze, ta ce Hannatu ta yi wannan roko ne bayan da ta ziyarci jarumin a asibitin da yake jinya da ke yankin Wuse a…
Read More
Zargin N17bn: Tinubu ya bada umarnin dakatar da binciken da ake yi wa Halima Shehu

Zargin N17bn: Tinubu ya bada umarnin dakatar da binciken da ake yi wa Halima Shehu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarni kan gaggauta dakatar da binciken da ake yi wa Shugabar shirin NSIPA, Halima Shehu. Kazalika, Tinubu ya amince da nadin Dokta Akindele Egbuwalo don maye gurbin Halima a matsayin mukaddashi. Idan za a iya tunawa, ‘yan watanni da suka gabata ne gwamnatin Tinubu ta nada Halima shugabancin NSIPA. Tun farko, rahotanni sun nuna hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tsare Halima a Talatar da ta gabata. An tsare ta ne jim kadan bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da ita daga mukaminta bisa zargin tura kudaden NSIPA Naira…
Read More
Kashi 70 na kudin Gadar Ɗan-agundi

Kashi 70 na kudin Gadar Ɗan-agundi

Daga MUHAMMAD SHAMSUDDEN Na karanta ra'ayoyi mabanbanta a kan wannan maganar, in da mafi yawan masu sharhi suka bayanna rashin gamsuwarsu da wannan tsari. Rubutun da suka fi daukar hankalina a dandalin Fesbuk su ne na Barista Abba Hikima da kuma na Malam Misbahu Baffa Na 'Yar Talla , ba kawai saboda zurfin iliminsu da hangen nesansu ba, a'a, saboda kokarinsu na tsage gaskiya da rashin siyasantar da abin da ya shafi al'umma. Dukkan wadannan kwararrru sun nuna rashin dacewar wannan tsari, duk da dai dan gajeren rubutu suka yi ba tare da cikakken sharhi ba, watakila saboda suna gudun…
Read More
IPPIS: Wasu mutane 6 da suka shaƙe wuyan ilimin jami’o’in gwamnati a Nijeriya

IPPIS: Wasu mutane 6 da suka shaƙe wuyan ilimin jami’o’in gwamnati a Nijeriya

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI Murnata daya, Buhari da ransa yana gani, an yi abin da gwamnatinsa ta sa aka lalata karatun jami'a da shi. Amma watakila cirewar ba wani cikakken amfani za ta yi ba, domin aikin gama dai ya riga ya gama. Yawancin jami'o'inmu a yanzu suna cikin tsananin wahala. Tsarin IPPIS din nan, da a ce an shirya adalci a cikinsa, ta hanyar cikashe wawaka-wawakan gibukan da ya zo da su, da kila ba shi da wata matsala, amma suna kallo mutanen jami'a suka ce zai cutar da mu, amma suka yi kememe, wai su ga masu mulki.…
Read More
Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a sabuwar shekarar 2024

Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a sabuwar shekarar 2024

Ya ku `yan uwana 'yan Nijeriya, ina cike da farin ciki a yayin da nake wa Ilahirinmu, matasa da tsofaffi maraba da shigowa sabuwar shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Dole ne mu daga hannuwanmu sama mu gode wa Allah Madaukakin Sarki saboda albarkar da Ya yi wa kasarmu da kuma rayukan mu a cikin shekarar da ta gabata wato shekara ta dubu biyu da ashirin da uku. Kodayake shekarar da ta gabata na kunshe da kalubale da dama, amma duk da haka an yi abubuwan alheri masu yawa, ciki har da mika mulki daga tsohuwa zuwa sabuwar…
Read More
Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta (2)

Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haduwa a wani makon a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu cigaba da tattaunawa a maudu'in da muka fara a makon da ya gabata. Wato yadda ake yawaitar samun  samari da 'yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Bayan kuma ba wani abu suka rasa da za a ce ana son su ba ko a aure su. A makon da ya gabata mun fara tattaunawa a kan wannan lamari har muka fara kawo muku wasu daga cikin dalilan da suke jawo haka, yanzu kuma…
Read More
Hizbah za ta fara kamen mabarata a titunan Katsina

Hizbah za ta fara kamen mabarata a titunan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Hizbah a Jihar Katsina ta bayyana cewar bada jimawa ba za ta fara kamen masu bara a duk fadin jihar. Shugaban hukumar Mallam Aminu Usman ( Abu Ammar) ne ya bayyana haka. A cewar shi gwamnatin jihar na yin dukkan mai yiwuwa don kawar da mabarata daga titinun jihar. "Bara ba ta daga cikin addini ta na kuma bata sunan addini da al'umarmu." Inji shi. Ya kuma bayyana cewar dokar da kafa hukumar Hizbah a jihar ta ba su damar shiga lungu da sako don cafko masu bara. "Idan mun kama su za mu…
Read More
An yi jana’izar mutane takwas da ‘yan bindiga suka hallaka a Katsina

An yi jana’izar mutane takwas da ‘yan bindiga suka hallaka a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata dabar 'yan ta'adda dauke da muggan makamai sun bude wa 'yan kasuwa takwas wuta, kusa da kauyen babangida bayan da suka dawo cin kasuwar Jibiya dake karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina. Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin. 'yan ta'addar sun kuma jikkata wasu karin mutane hudu a yayin da wasu biyu suka vata tun bayan harin da aka kai jiya Lahadi da dare. Wadanda aka kashe din mazauna kauyen 'Yan gayya ne a karamar hukumar ta Jibiya dake makota da Zurmi ta jihar Zamfara. Rahotanni sun bayyana cewar…
Read More
‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga yankin Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa sun ce, 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban hukumar, Mr. Safiyanu Isa Andaha. Hadimin Gwamnan jihar kan lamurran kananan hukumomi da masarsutu, Haruna Kassimu ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace Safiyanu Isa ne a kauyen Ningo da ke hanyar Akwanga - Andaha a yankin. Ya kara da cewa, an sace shugaban karamar hukumar ne tare da wani mai suna Alhaji Adamu Tanko Custom da misalin karfe 8:30 na daren Litinin da ta gabata. Kazalika, Kassimu ya ce jami'an tsaro sun dukufa bincike…
Read More