Daga UMAR GARBA a Katsina
Hukumar Hizbah a Jihar Katsina ta bayyana cewar bada jimawa ba za ta fara kamen masu bara a duk fadin jihar.
Shugaban hukumar Mallam Aminu Usman ( Abu Ammar) ne ya bayyana haka.
A cewar shi gwamnatin jihar na yin dukkan mai yiwuwa don kawar da mabarata daga titinun jihar.
“Bara ba ta daga cikin addini ta na kuma bata sunan addini da al’umarmu.” Inji shi.
Ya kuma bayyana cewar dokar da kafa hukumar Hizbah a jihar ta ba su damar shiga lungu da sako don cafko masu bara.
“Idan mun kama su za mu tantance wadanda ke da bukatar taimako mu mika su ga hukumar zakka da wakafi don a taimake su.
“Gwamna Dikko Radda ya kafa hukumar zakka da wakafi don taimakon masu bukata,” inji shi.
Ya ja hankalin iyaye da sauran al’uma a jihar akan su kula da yaransu, a cewarsa gwamnati baza ta ci gaba da lamuntar aiyukan rashin tarbiya ba.
“Babu iyayen da za su zura ido su ga ‘yayansu na shaye shayen miyagun kwayoyi, saboda haka iyaye su hada kai da mu don inganta rayuwar matasan jihar nan.” Inji shi.
Daga karshe ya yi kira ga al’uma akan su fallasa dukkan wuraren da ake aikata babala a jihar.
