Hannutu Musawa ta buƙaci a tallafa wa jarumi Zack Orji kan jinyarsa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Ministar Kirkire-kire da Al’adu, Barista Hannatu Musawa, ta yi kira ga masu hali a Nijeriya da su dubi Allah su taimaka wa jarumin masa’antar Nollywood, Zack Orji, bisa jinyar da yake yi a halin yanzu.

A ranar Litinin da ta gabata aka yi wa jarumin aiki na lalurar da yake fama da ita mai nasaba da kwakwalwa.

Wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun hadimarta, Nneka Ikem Anibeze, ta ce Hannatu ta yi wannan roko ne bayan da ta ziyarci jarumin a asibitin da yake jinya da ke yankin Wuse a Abuja.

“Allah zai ba shi lafiya. Za mu yi bakin kokarinmu wajen tallafa masa. Muna kira ga ‘yan Nijeriya da mu taimaka masa da addu’a, saboda tamkar dangi yake a gare mu.

“Mun kalli yadda ya nishadantar da mu. Muna kallonsa a matsayin jigo a kasa. Don haka, gatan da za mu yi masa, shi ne mu yi bakin kokarinmu wajen tallafa masa samun kyakkyawar kulawa,” in ji Hannatu.

Hannatu ta kara da cewa, “Za mu tutunbi masu hali a kasa don su shigo su tallafa wa Zack Orji ta hanyar addu’o’i da sauransu domin tabbatar da ya samu lafiya.”

By Editor