A yanzu ana kallon marubuci kamar wanda bai san kansa ba – Ayusher Muhammad

“Kaso sittin bisa ɗari Ina wa rubutu kallon sha’awa ne”

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Aisha Muhammad Salis, wadda aka fi sani da Ayusher Muhammad a harkar rubutun onlayin, ta na daga cikin fitattun marubutan soshiyal midiya da a yanzu ake yayin su.

Haka kuma tana da basira da salon kirkirar labari da rubutawa. Don haka ne ma ta yi fice a cikin marubutan da ake ji da su a onlayin.

Domin jin ko wacece Ayusher, wakilin Blueprint Manhaja a Kano, ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Da farko dai za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.

AYUSHER: Assalamu alaikum. Da farko dai sunana A’isha Muhammad Salis, wacce aka fi sani da sunan Ayusher Muhammad.

Ni ‘yar asalin ‘yar Jihar Jigawa ce a Karamar Hukumar Gwaram. Mahaifina ya koma Kaduna da aiki, inda a nan na yi ‘Primary School’ di na a ‘Abubakar Gumi College’, na kuma yi sauka a Hayatul Islam.

Bayan na gama ne na tafi makarantar ‘Unity College’ Kachako, inda na yi ‘Secondary School’ di na a can. Na gama karatu na a shekarar 2011 na kuma yi aure a 2013.

To, bayan na yi aure ne na ci gaba da karatu na a makarantar ‘Informatics’ da ke Kazaure, na kammala ‘advance diploma in computer science’.

Ya aka yi ki ka samu sunan da aka san ki da shi a rubutu, kuma menene ma’anar sa?

Ayusher Muhammad, da wannan sunan aka san ni a harkar rubutu. Maganar gaskiya na saka sunan ne a farko don na voye ni ce mai rubutun, don a farko ina tantama a kan labarin da na ke rubutawa a kan ba zai karbu ba. Sai na lankwasa sunan daga baya kuma sai sunan ya bi ni.

Yaushe ki ka fara rubutu, kuma ya aka yi ki ka samu kanki a cikin harkar?

To, ni dai na fara rubutu a shekarar 2015, sannan na fara rubutu ne sakamakon karance-karancen ‘Novels’ da na ke yi irin na ‘published’ da ake yi. To, lokacin da aka fara rubutun onlayin, sai na fara tunanin kamar fa ni ma zan iya. To, kawai ranar kamar wasa na gwada tura shafi daya a group din da na ke ciki, na yi mamaki sosai da na ji wasu su na neman ci gaban labarin, wanda kuma daga haka ne na kai inda na kai yanzu.

Kin taba yin rubutun littafi, ko dai da na onlayin ki ka fara? Idan ba ki taba rubutun littafi ba ko ki na da sha’awar nan gaba ki yi?

Gaskiya ban tava rubutun littafi na takarda da ake wallafawa ba, da na onlayin na fara, har kuma yanzu da shi na ke amfani. Kuma a yanzu dai ba ni da sha’awa gaskiya, na yi rubutun littafin da zan buga, don in mu ka duba za mu ga su kan su masu wallafawar onlayin din dai suke dawowa, wannan ya na daya daga cikin canji da aka samu na ci gaba wanda abubuwa da dama ta wayar hannu ake amfani da shi. Mutane su na ganin me zai sa su sayi littafi ruwa ya jika shi ko su siya yara su yaga shi, ga inda yake a wayar su duk inda su ka shirya sai dai su bude su karanta. To, wannan dalilin ya sa na san ba zan iya wallafa littafi ba. Gaskiya sai dai ko nan gaba in ra’ayi ya canza.

A matsayin ki ta marubuciya ko yaya za ki kwatanta rayuwarki ta baya da kuma ta yanzu da ki ke rubutun da mutane suke karantawa?

Hmm! To, a gaskiya da ka ga daga ni sai wadanda na sani. Amma zama na marubuciya ya sa mutane da yawa su ka sanni, na kuma hadu ni ma da mutane da yawa na kwarai wanda mu ke zumunci na ke kuma jin su kamar ‘yan’uwa na.

Abu na biyu kuma, ina ji kamar ina kyautatawa ta wani vangaren ta hanyar isar da saqon da na ke son na isarwa wanda za ka ga mutane da dama su na biyo ni su ce tabbas sun ji dadin rubutun nan sun kuma gode da ilimantarwa da nishadantarwa. Ka ga wannan ma wani abu ne na jin dadi.

Me ki ka dauki harkar rubutu a rayuwarki, sana’a ko dai sha’awa?

To, in na ce duka biyu ai ban yi zari ba ko? A gaskiya ni a sha’awa na dauke shi kuma har yanzu kashi sittim a cikin dari a sha’awar yake, sai dai in mu ka duba ta wani vangaren za mu ga kowa ya na ci gaba don me mu za mu yi ta zama a haka? Bayan ga baiwa Allah ya ba mu wanda za mu iya amfani da ita mu yi sana’a daga gida.

Mun yi rubutu da a kyauta ka ga yanzu in mu ka ce sana’a mu ke to a gani na mutane kamata ya yi su taya mu karfafa gwiwa don mu ma aikin da mu ke ba mai sauqi ba ne, to kuma Alhamdu llilah mu na samu ta hanyar rubutu wanda hakan ke nuna mana mutane na fahimtar mu.

Ko akwai wasu nasarori da ki ka samu a cikin harkar rubutun ki?

To, Alhamdu llilah na samu nasarori wanda sai dai hamdala da gode wa Allah. Sannan mu na fatan mu ma nan gaba rubutun mu masu wasan kwaikwayo su rinka saya su na amfani dashi ta hanyar yin wasanin su na kwaikwayo kamar yadda wasu kasashe da dama ke yi.

Wani buri ki ke so ki cimma a harkar rubutu? Kuma burin na ki ya cika ko sai nan gaba?

To gaskiya na cika rabi saura rabi. Rabin da na cika shi ne Alhamdu llillah, na yi rubutun labarurrukan da har yau in ina saurara ni kai na ina jin dadin su, ina kuma alfahari da ni ce na rubuta su.
Sannan ina fatan nan gaba rubutun da mu ke yi ya je inda ya kamata. Sauran burukan kuma ina rokon Allah ya cika mini su.

Wasu irin matsaloli marubuta suke fuskanta a wannan lokacin?

To, maganar gaskiya mu na fuskatantar qalubale da yawa, idan ka duba yadda ake daukar marubuci yanzu kamar wani wanda bai san kan sa ba. Sai ka ga wata ta na zaune a gida haka kawai ta tsaro zagi da cin mutunci ta makala sunan ka, babu abin da ka yi mata balle ka sa ran ramuwa ta yi, wata kuwa haka za ka ga kawai don ba ta yin rubutun ka ta je guri ta na zagi da ci maka mutunci. Balle uwa, uba yi mana hassada da ake yi. Wani a duniya shi kuma baqin cikin sa bai wuce ya ga mun ci gaba ba. To wannan kadan ne daga qalubalen da mu ke samu.

Menene sakon ki ko kiran ki ga abokan harkar ki ta rubutu?

To, ni dai sako na ba zai wuce daya zuwa biyu ba, da farko dai mu san me mu ke yi, mu kuma san me mu ke rubutawa. Shi rubutu kamar abu mai rai ne, zai bi mu har qarshen rayuwar mu, kada ki ga wai ki na daga gida ki na rubuta abin da ran ki ya so, ba kya tsayawa ki yi duba da qima da mutuncin ki, ba kya tsayawa ki yi duba da wanda zai karanta.

Babu shakka yadda ya tafi zai dawo mana. Domin ko rasuwa mutum ya yi, wani da wannan abin zai iya tuno shi.

Sannan mu sani rubuta abin da zai jefa wani halaka, babbar halaka ce kaima a tattare da kai domin kaima kana da kamasho na lalacewar wannan mutumin, duk kuma halin da wani ya fada saboda kai to fa ka san kaima ka na da na ka kamashon.

Allah ya ba mu ikon ci gaba da rubutu mai amfani wanda zai ilimantar ba wai ya gurbatar ba.

To, madalla mun gode.

Ni ma na gode.