05
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta sanar da tsawaita wa’adin rufe karbar kudaden aikin Hajjin bana. A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan sashin hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Talata, NAHCON, ta dage wa’adin zuwa 31 ga watan Janairu. Ta ce karin wa’adin ya biyo bayan koke-koken da malaman addini da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki kan a tsawaita wa’adin. A cewar Usara, duba da kiraye-kirayen da dumbin al’umma suka yi kan tsawaita wa’adin ya nuna bukatar samar da dama ga…
