Editor

9513 Posts
Jagora ya yaba wa Hamisu Ibrahim kan rubuta littafin koyar da Larabci da Turanci

Jagora ya yaba wa Hamisu Ibrahim kan rubuta littafin koyar da Larabci da Turanci

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Kwamared Adam Abubakar Adam wanda aka fi sani da Jagora, daya daga cikin jagororin Kungiyoyin Ci Gaban Al'umma a Karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano ya yaba wa hazikin marubucin nan Malam Hamisu Ibrahim wanda ya bada gudunmawa wajen rubuta littafi wanda ya kunshi kalmomin Larabci zuwa Turanci domin amfanin masu son koyon Larabci tun daga tushe kamar dai yadda Jagoran ya bayyana cewa wannan ba karamin aiki ba ne da zai taimaka wa wadanda suka san Turanci su koyi Larabci a matakin farko. Jagora ya kara da cewa "akwai bukatar marubutanmu su yi amfani da…
Read More
Luiz Suarez ya bi sahun Messi zuwa Inter Miami ta Amurka

Luiz Suarez ya bi sahun Messi zuwa Inter Miami ta Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dan wasan gaban Uruguay Luiz Suarez ya koma Inter Miami ta da ke aasar Amurka, inda zai sake haduwa da tsoffin abokan wasansa na Barcelona Lionel Messi, Sergio Busquets da Jordi Alba. Suarez, wanda shi ma ya lashe kofunan lig da Nacional da Ajax da kuma Atletico Madrid, ya zura kwallaye 17 a wasanni 33 yayin da Gremio ta kare a matsayi na biyu a gasar Seria A ta Brazil a kakar wasa ta 2023. Bajintar dan wasan na daga cikin abin da ya sanya aka zave shi a matsayin gwarzon dan wasa a gasar. Amma…
Read More
Sauyin yanayi: Ƙalubalen da wasu garuruwa ke fuskanta a Jihar Yobe

Sauyin yanayi: Ƙalubalen da wasu garuruwa ke fuskanta a Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya ta fitar a 2019 ya bayyana cewa Nijeriya ta na asarar kimanin fili mai fadin murabba'in kadada 350,000 a duk shekara, sakamakon yadda hamada ke ci gaba da mamayewar yankuna, wanda hakan ya na faruwa ne ta musababbin sauyin yanayi, mai alaka da ayyukan yau da kullum da Dan Adam masu jawo dumamar yanayi. A nata bangaren, a wani sabon binciken da Hukumar Agora Policy ta gudanar a wannan shekara (2023), ta bayyana cewa, Nijeriya za ta iya yin hasarar Dalar Amurka kimanin biliyan 460 sakamakon sauyin…
Read More
Mutane za su ƙara shiga wahala a wasu yankunan Arewacin Nijeriya – Bankin Duniya

Mutane za su ƙara shiga wahala a wasu yankunan Arewacin Nijeriya – Bankin Duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bankin Duniya ya yi hasashen za a ci gaba da samun tabarbarewar matsalar tsaro da rikicin 'yan bindiga da matsin rayuwa a kananan hukumomin jihohin Borno da Kaduna da Katsina da Sakkwato da Yobe da Zamfara da kuma Adamawa har zuwa watan Mayun 2024. Hasashen bankin na zuwa ne daidai lokacin da ya bayyana cewa rashin nagartattun tsare-tsaren tattalin arziki sun haifar da raguwar samun amfanin gona a Nijeriya. Wannan dai zai shafi batun samar da hatsi a kasar. Bankin Duniyar ya bayyana haka ne a rahoton baya-bayan nan da ya fitar game da…
Read More
An kafa hukumar KSCHMA don taimakekeniyar lafiya ga ɗaukacin al’ummar Kano – Dr Rahila

An kafa hukumar KSCHMA don taimakekeniyar lafiya ga ɗaukacin al’ummar Kano – Dr Rahila

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano An bayyana cewa an kafa Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ne domin amfanin daukacin al'ummar Jihar Kano, ba wai ma’aikata kawai ba. Hukumar ta KSCHMA an kafata ne don taimakekeniyar kula da lafiyar ma’aikatan gwamnati da kamfanoni da ma daukacin al'umma ba lallai sai ma'aikacin gwamnati ba. Hukumar ta taimakekiniyar lafiya kowa zai iya yin rajista domin kula da lafiyarsa da ta iyalinsa gwargwardon yadda doka da yarjejeniyar wannan hukuma ta tanada na kula da lafiyar al'umma ta hanyar taimakekeniya. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugabar hukumar ta Jihar Kano Dr Rahila Mukhtar inda ta…
Read More
Rasuwar Ambasada Anka babban rashi ne ga Zamfara – Gwamna Lawal

Rasuwar Ambasada Anka babban rashi ne ga Zamfara – Gwamna Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyya dangane da rasuwar dattijon kasa, Ambasada M.Z Anka, tare da bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Zamfara. A ranar Juma'a Allah Ya yi wa marigayin cikawa. Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fada cikin sanarwar da ya fitar ran Juma'a cewa, Gwamna Lawal ya ce rasuwar Ambasada Anka ta haifar da wagegen gibi saboda kwarewarsa. A cewar Gwamnan, "Ba ahalin Ambasada M.Z Anka kadai ke alhinin rasuwarsa ba, har ma da al'ummar Jihar Zamfara baki daya. "Marigayi Anka ya yi rayuwa abar koyi, mai cike da kyawawan dabi'u…
Read More
‘Yan bindiga sun yi barazanar sake kai hari a Filato

‘Yan bindiga sun yi barazanar sake kai hari a Filato

Daga BASHIR ISAH ‘Yan bindiga sun yi barazanar sake kai sabon hari a kauyen Jihar Filato kwana hudu da kai hare-hare a wasu sassan jihar wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutum 195. Mataimakin Sakatare na kasa na kungiyar Middle Belt Forum, Stanley Kavwam, shi ne ya bayyana haka a tattaunar da aka yi da shi a tashar Arise Television a ranar Alhamis. A cewarsa, ‘yan bindigar sun aike da wasikar sanarwa kan za su kai hari a kauyen Pushit da ke yankin Karamar Hukumar Mangu a jihar. Da yake amsa tambaya kan batun, Mai magana da yawun ‘yan sandan…
Read More
Shettima ya yaba wa Gwamna Sule kan tabbatar da zaman lafiya a Nasarawa

Shettima ya yaba wa Gwamna Sule kan tabbatar da zaman lafiya a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiya Abdullahi Sule, bisa tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar, tare da jaddada cewa cigaban al’umma ba ya samuwa sai da zaman lafiya. Shittima ya yi wannan yabo ne a yayin da yake kaddamar da hanya mai tsawon kilomita 5 da Gwamna Sule ya gina a yankin Masaka-Luvu, a Karamar Hukumar Karu da ke jihar a ranar Alhamis. Mataimakin Shugaban Kasar ya ce abin a yaba ne ainun yadda Gwamna Sule ke ci gaba da tabbatar  da zaman lafiya a jiharsa duk da irin…
Read More
Emefiele ya nesanta kansa daga zarge-zargen talauta Nijeriya

Emefiele ya nesanta kansa daga zarge-zargen talauta Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya karyata zargin da Mai Binciken CBN Na Musamman da Shugaba Bola Tinubu ya nada ya yi masa, wato Jim Obazee. Kwanan nan Obazee ya gabatar wa Tinubu rahoton harqallar da ya bankado Emefiele ya aikata a CBN, wadda aka yi zargin ya bindige biliyoyin nairori da biliyoyin daloli. Cikin harkallar da Obazee ya bankado har da badakalar sauya launin kudi, wadda Obazee ya ce damfara ce kawai sata Emefiele ya kantara. Da ya ke karyata zarge-zargen da Obazee ya yi masa Emefiele a ranar Lahadi…
Read More
Haƙƙin tabbatar da zaman lafiya ya rataya a kanmu ne duka – Tinubu ga gwamnoni

Haƙƙin tabbatar da zaman lafiya ya rataya a kanmu ne duka – Tinubu ga gwamnoni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi gaba daya ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar. Da yake jawabi yayin wata ganawa da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a gidansa da ke Legas ranar Talata, shugaban ya sake yin Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato. Da yake jawabi ga gwamnonin, shugaban ya bayar da wani kakkausan umarni ga jami’an tsaro da su dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Filato tare da kara zage damtse wajen zaqulo wadanda suka…
Read More