Editor

9513 Posts
Gobara ta ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukumar Ɗandume

Gobara ta ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukumar Ɗandume

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gobara ta kone mafi yawan ofishoshin sakatariya na Karamar Hukumar Dandume a jihar Katsina.    Gobarar da ta tashi da yammacin ranar Lahadi da ta wuce ta kone ofishoshi 31na sakatariyar.                 Wasu a cikin ofishoshin da suka kone sun hada da na Shugaban Karamar Hukumar da na ofishin jagoran kansiloli da kuma dakin taro na karamar hukumar.                   Sauran sun hada ofishin baitul mali da na wasu kansiloli.                           Haka kuma akwai ofishin Daraktan ma'aikata da na mai biciken kudi duk na karamar hukumar sun kone kurmus. Da yake duba ofishoshin da gubarar ta lashe shugaban karamar…
Read More
Tarihi da siyasar rayuwar Ghali Umar Na’Abba

Tarihi da siyasar rayuwar Ghali Umar Na’Abba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haife shi ne a gidan Umar Na’Abba, babban dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958. Mahaifinsa ya kasance mai karfin tarbiyya kuma malamin addinin Musulunci. Mahaifinsa ya koya masa kyawawan halaye na aiki tukuru, kasuwanci, sahihiyar magana, jajircewa, halin sassaucin ra'ayi, hankali, ladabi da son addini sosai. Ilimi: Ya yi makarantar firamare ta Jakara da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1969, sannan ya halarci Kwalejin Rumfa da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatu ta Afirka ta Yamma. A tsakanin…
Read More
Harin Filato: Ku ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki – Sarkin Musulmi ga gwamnati

Harin Filato: Ku ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki – Sarkin Musulmi ga gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan harin da aka kai jihar Filato, inda aka kashe sama da mutane 155 a jajibirin Kirsimeti. Ya yi kira ga gwamnati da ta wuce yin Allah wadai da hare-haren tare da inganta matakan tsaro. Ya yi wannan jawabin ne a wajen rufe taron koyar da sana’o’in addinin musulunci karo na 8 da aka gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa a ranar Larabar da ta gabata, wanda kungiyar dalibai musulmi ta Nijeriya, MSSN ta shirya. Da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar tavarvarewar tsaro a…
Read More
‘Yan sanda sun cafke ɗalibar da ke kai wa ’yan bindiga rahoto

‘Yan sanda sun cafke ɗalibar da ke kai wa ’yan bindiga rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An cafke wata dalibar Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Kontagora, kan zarginta da kai wa ’yan bindiga bayanai a Jihar Neja. Kwamishinan ’yan sandan Jihar Neja, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ce an cafke dalibar da ke karatu a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da ke Kontagora ne bayan an kama wani dan bindiga mai shekara 37. A yayin binciken dan bindigan da aka kama a garin Kontagora ne aka gano lambar dalibar a cikin wayarsa. Ita kuma a wurin bincike aka gano sunan wani dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Shaibu Haruna a…
Read More
Ɗan majalisa ya tallafa wa makarantar Islamiyya a Funtuwa

Ɗan majalisa ya tallafa wa makarantar Islamiyya a Funtuwa

Daga DAUDA USMAN a Legas Dan malalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Funtuwa a zauren majalisar jihar Katsina Hon, Abubakar Muhammed Total Funtuwa kuma Shugaban Kwamitin Lafiya a majalisar jihar Katsina ya bai wa wata makarantar Islamiyya a mazabarsa mai suna Anwaruddin Islamic Centre Funtuwa gudunmawar kudi har Naira dubu dari biyar a matsayin gudunmawar da makarantar take nema a hannuwan al'ummar Musulmi domin ara fadada ajijuwan makarantar baki daya. Dan majalisar dokokin na jihar Katsina Hon, Abubakar Muhammed Total Funtuwa ya bai wa makarantar wannan gudummawar ce a Funtuwa a lokacin da makarantar ta Anwaruddin Islamic Centre…
Read More
Rasuwar Ghali Na’abba babban rashi ne ga ƙasar nan – Ɗanpass

Rasuwar Ghali Na’abba babban rashi ne ga ƙasar nan – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Fitaccen dan kasuwa basarake Dan-Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya bayyana mutukar alhininsa bisa rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilalai na Nijeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba. Ya bayyana cewa rasuwar Ghali babban rashi ne ba ga jihar Kano kadai ba har ma da Arewa da kasa baki daya. Sannan fitaccen dan siyasa ne wanda ya yi gwagwarmaya domin tabbatar da adalci a tsarin tafiyar da dimukradiyyar kasar nan. Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya ce a lokacin da yake kakakin majalisar wakilai kowa ya shaida a kasar nan, bai zama dan kanzagi ko dan amshin…
Read More
Tsofaffin ɗaliban makarantun kimiyya na Kano sun yi aniyar samar da jami’a

Tsofaffin ɗaliban makarantun kimiyya na Kano sun yi aniyar samar da jami’a

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar tsofaffin dalibai na makarantun kimiyya na jihar Kano sun ci alwashin samar da jami'a ta kungiyar. Sabon Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Balarabe Jallah ne ya bayyana haka a jawabinsa na karbar jan ragamar kungiyar bayan rantsar da su a taron shekara da kungiyar ta gudanar a Jami'ar Bayero. Ya ce duba da yawan da suke da shi na 'yan kungiyar ya kamata a ce sun jawo hankalin masu ruwa da tsaki domin yara da suke fitowa daga makarantun kimiyyar da su rika fita waje suna karatu idan jami'ar ta samu za ta taimaka…
Read More
Duk wanda ya zama abin sha’awa a duniya mace ce ta mayar da shi hakan – Mariya Durumin Iya

Duk wanda ya zama abin sha’awa a duniya mace ce ta mayar da shi hakan – Mariya Durumin Iya

"Rayuwar maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya" Daga AISHA ASAS Rayuwar aure rai ne da ita tamkar dai yadda aka san dan adam da ruhinsa, yayin da mai shar'antawa Ya yi kira, ruhinsa ba zai kara ko sa'a daya a jikin ba, zai fice yana mai amsa kiran mahallici. Idan kuwa ba shi ya yi kiran nasa ba, ko duniya za ta taru don ganin ta tsayar da numfashinsa ba za ta iya tsayar da shi ba. Haka ita ma rabuwar aure, daga auren har ranar karewar sa rubatacce ne, idan ranar rabuwa ta zo,…
Read More
Gobe majalisun tarayya za su yi zaman ƙarshe kan Kasafin 2024

Gobe majalisun tarayya za su yi zaman ƙarshe kan Kasafin 2024

Daga BASHIR ISAH Gobe Juma'a ake sa ran sanatoci da 'yan majalisar wakilai za su yi zama domin amincewa da kasafin 2024 wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar musu. Sanata Opeyemi Bamidele, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin a Jihar Ekiti. Sanatan ya ce dukkan 'yan majalisun tarayya za su katse hutunsu domin yin wannan inda za a amince da kasafin 2024. “Don tabbatar da an amince da kasafin a kan lokaci, ya sa muka bukaci baki daya ma'aikatu da hukumomi su bayyana gaban hadakar kwamitocin Majalisar Dattawa da ta walakilai. “Wanda hakan ya…
Read More
Tarihin Alhaji Musa Ɗan Ƙwairo

Tarihin Alhaji Musa Ɗan Ƙwairo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhaji Musa Dan Kwairo ya kasance fitaccen mawakin kasar Hausa kuma mai matukar daraja. An haife shi ne a garin Bakura na Jihar Zamfara a Nijeriya a farkon shekarar 1909. Hazakar Musa Dan Kwairo ta fannin waqa da sha’awar wakokin gargajiya ta fito ne tun yana karami, kuma zai cigaba da zama daya daga cikin fitattun jarumai a wannan fanni. Wakar gargajiyar Hausa tana da matukar muhimmancin al’adu a yankin arewacin Nijeriya, kuma Musa Dan Kwairo ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyayewa da kuma habaka wannan al’adun gargajiya. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen samar da kyawawan…
Read More