Harin Filato: Ku ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki – Sarkin Musulmi ga gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan harin da aka kai jihar Filato, inda aka kashe sama da mutane 155 a jajibirin Kirsimeti.

Ya yi kira ga gwamnati da ta wuce yin Allah wadai da hare-haren tare da inganta matakan tsaro.

Ya yi wannan jawabin ne a wajen rufe taron koyar da sana’o’in addinin musulunci karo na 8 da aka gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa a ranar Larabar da ta gabata, wanda kungiyar dalibai musulmi ta Nijeriya, MSSN ta shirya.

Da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar tavarvarewar tsaro a Nijeriya, Sarkin Musulmi ya nuna shakku kan tashe-tashen hankula da asarar rayuka a kasar.

Ya kuma jaddada buqatar daukar matakan dakile irin wadannan hare-hare, tare da kara nuna damuwa kan ingancin hanyoyin tattara bayanan sirri.

Don haka ya bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Ya jaddada muhimmancin amincewa da shugabanci tare da yin kira da a hada kai ta fuskar addini.

A cikin roko ga shugabanni, Sarkin Musulmi ya yi kira da a hada karfi da karfe domin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar al’umma, yana mai bayyana cewa lokacin barci ya wuce.

Ya ce: “Kullum muna yin Allah wadai da irin wadannan abubuwa amma bayan mun yi Allah wadai da irin wadannan ayyukan da wadannan ‘yan fashi da muggan laifuka ke yi, sai me kuma?

“Mene ne aikin gwamnati da ya kamata ta kare rayuka da dukiyoyi? Me ya sa ba za mu kasance masu kwazo ba kuma mu dakatar da irin wadannan hare-haren kafin su faru? Me ya faru da tsarin tattara bayananmu.”