Editor

9513 Posts
An gurfanar da Hafsat ‘Chuchu’ kan zargin kisan Nafiu Hafiz

An gurfanar da Hafsat ‘Chuchu’ kan zargin kisan Nafiu Hafiz

*Ta musanta zargin da ake yi mata Daga BASHIR ISAH An gurfanar da Hafsat Surajo wadda aka fi sani da Chuchu, bisa zargin kashe abokin kasuwancinta, Nafiu Hafiz, a Kano. Duk da dai da fari Hasfat ta yi ikirarin ita ce ta kashe marigayin, amma ta musanta zargin da ake yi mata yayin zaman sauraren shari'a da kotu ta yi a ranar Laraba. An maka Hafsat a Kotun Chief Magistrate No. 37 ne da ke yankin Yankaba, Kano, inda ake zargin ta kashe Nafiu Hafiz. Mai magana da yawun 'yan sanda a Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa, ana…
Read More
Cin amanar makusanta ga cin zarafin ’ya’ya mata

Cin amanar makusanta ga cin zarafin ’ya’ya mata

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na samu halartar wani taron kaddamar da littafin da wata matashiyar marubuciya ta wallafa da harshen Turanci, mai suna Shackles of Abuse, wato Sarkakiyar Cin Zarafi, labarin bautar da ’ya’ya mata cikin lalata. Ko da yake ba ina son yin sharhi kan littafin ba ne, sai dai labarin da jigon littafin ya tavo ne ya tava zuciyata, kuma na ga ya dace mu yi nazari a kansa cikin wannan mako. Labaran da ke cikin wannan littafin suna da tsoratarwa da firgitarwa ainun, musamman irin yadda marubuciyar ta rika kwatanta halin da ta samu kanta a…
Read More
An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon Gwamnan Ondo sa’o’i bayan rasuwar Akeredolu

An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon Gwamnan Ondo sa’o’i bayan rasuwar Akeredolu

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki, an rantsar da Mukaddashin Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin sabon gwamnan jihar. A ranar Laraba da misalin karfe 5:20 na yamma aka rantsar da sabon Gwamnan wanda Babban Alkalin Jihar, Mai Shari'a Olusegun Odusola ya jagoranta. Rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon Gwamnan Ondo ya biyo bayan rasuwar Gwamnan Jihar ne, Rotimi Akeredolu, wanda Allah Ya yi wa cikawa ranar Laraba a wani asibitin Jamus. Rantsarwar ta yi daidai da tanadin Kundin Tsarin Mulki na kasa na 1999 (wanda aka gyara) gudun kada a bar wani gibi a shugabancin jihar.…
Read More
Ba zan iya cewa ga mutum ɗaya da ya shigo da ni harkar fim ba – Hajara Yusuf Makama 

Ba zan iya cewa ga mutum ɗaya da ya shigo da ni harkar fim ba – Hajara Yusuf Makama 

DAGA MUKHTAR YAKUBU Idan Allah ya kaimu ranar 26 ga Disamban nan za a nuna Fim din Pricenss Of Galma na kamfanin Jammaje Production a katafaren dakin taro na Musa Abdullahi da ke harabar sabuwar Jami'ar Bayero da ke Kano wanda ake sa ran dubun dubatar mutane za su halarta domin kallon wannan fim din da ya zamo zakaran gwajin dafi a cikin finafinan Kannywood. Jarumar Kannywood Hajara Yusuf Makama na daya daga cikin jarumai masu tasowa da a ke ganin zuwa nan gaba kadan za ta kai matakin manyan jaruman da ake ji da su a Kannywood, ita ce…
Read More
Shugaba Tinubu, Dila Sarkin Wayo!

Shugaba Tinubu, Dila Sarkin Wayo!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Kamar yadda mai ba da shawara na musamman kan siyasa ga shugaba Tinubu wato Alhaji Ibrahim Masari ya radawa shugaban suna Bala Tanimu Ashiru, ni kuma ga wasu matakan da shugaban ke Dauka ina son na yi ma sa kirari ne da zama DILA SARKIN WAYO don la'akari da yadda ya ke tinkarar lamuran Kasar tun lokacin da ya hau karaga a ranar 29 ga watan Mayu. Dama 'yan Nijeriya na cikin Kuncin tattalin arziki lokacin da ya hau karaga don haka cire tallafin man fetur da ya yi bai zama abun mamaki ba don…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya rasu

Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya rasu

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya rasu a safiyar Laraba bayan fama da rashin lafiya. Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa, Gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 67, bayan shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da kansar mafitsara. Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan Gwamna Akeredolu ya rubuta wasikar tafiya neman lafiya, inda ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa. Marigayin ya shafe kusan wata uku a kasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Nijeriya a watan Satumban…
Read More
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na’Abba ya kwanta dama

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na’Abba ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa, Alhaji Ghalli Na’abba rasuwa. Duk da dai babu cikakken bayani game da rasuwar tasa, amma majiya mai tushe ta ce marigayin ya rasu ne da misalin karfe 3:00 na daren da ya gabata. A shekarar 1999 ya zama dan majalisa mai wakiltar Kano Municipal a Majalisar Wakilai, inda daga bisani ya samu nasarar zama Kakakin Majalisar. An haifi marigayin ne a 1958 a zuri'ar Alhaji Umar Na’Abba, a yankin Tudun Wada, Kano.
Read More
Rashin Tsaro: Mu koma ga Allah don samun mafita – Sanata Yari

Rashin Tsaro: Mu koma ga Allah don samun mafita – Sanata Yari

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sanata Abdulaziz na jihar Zamfara ya ce mafita daya tilo da za a magance tabarbarewar tsaro a yankin Arewa shi ne komawa ga Allah. Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga dukkanin kananan hukumomin jihar 14 a gidansa da ke garin Talata Mafara, hedikwatar karamar hukumar Talata Mafara a ranar Talata. Sanata Yari mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa ya koka da cewa, duk da kokarin da aka yi wanda ya hada da tattaunawa da ‘yan ta'adda da sauran hanyoyin da…
Read More
Za mu bunƙasa haɗin kai a ƙungiyar kamfanin tsaro masu zanan kansu a Kano – Dakta Idris

Za mu bunƙasa haɗin kai a ƙungiyar kamfanin tsaro masu zanan kansu a Kano – Dakta Idris

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar Kamfanin Tsaro Masu Lasisi Masu Zaman Kansu na Nijeriya, reshen Jihar Kano ta zabi sabbin shugabanni a zaben da aka gudanar a harabar hukumar jami'an tsaro masu kulada fararen hula na jihar Kano. An  yayin zaben an zabi Dakta Idris Adamu Pukuma shugaban kamfanin tsaro na Pama Global Security a matsayin shugaban kungiyar ba  tare da hamayya ba, sannan an  zavi  Alhassan Bello Samsam   a matsayin mataimakin shugaba da Mista.Williams  Michael na kamfanin tsaro na  "Original Security "a matsayin sakatare janar na kungiyar da sauran wadanda aka  zaba a mukamai daban-daban na kungiyar. Da…
Read More
Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta

Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haDuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini Blueprint Manhaja. A wannan maudu'i da za mu tattauna a wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun  samari da 'yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Kasashen Hausa cike suke da wadannan matsaloli. Kuma kowa ka tava cikin wadannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure…
Read More