Rashin Tsaro: Mu koma ga Allah don samun mafita – Sanata Yari

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Abdulaziz na jihar Zamfara ya ce mafita daya tilo da za a magance tabarbarewar tsaro a yankin Arewa shi ne komawa ga Allah.

Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga dukkanin kananan hukumomin jihar 14 a gidansa da ke garin Talata Mafara, hedikwatar karamar hukumar Talata Mafara a ranar Talata.

Sanata Yari mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa ya koka da cewa, duk da kokarin da aka yi wanda ya hada da tattaunawa da ‘yan ta’adda da sauran hanyoyin da Gwamnatin Tarayya da na jihohi suka dauka kan matsalar rashin tsaro, matsalar rashin tsaro na karuwa a wasu jihohin arewacin kasar.

“Duk da kokarin da gwamnati ke yi kan matsalar rashin tsaro a wasu yankunan Arewa, mun lura da cewa lamarin yana kara ta’azzara kuma mafita daya tilo na ayyukan ‘yan ta’addan da suka addabi yankin shi ne a koma ga Allah Madaukakin Sarki domin neman taimakon Allah,” in ji Yari.

Ya kuma yi kira ga malaman addini da su rika yin addu’o’in samun zaman lafiya a yankin.

A cewarsa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen magance duk wani nau’in ta’addanci a kasar nan.

Ya kuma bukaci ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayansa da su kasance masu bin doka da oda a jihar domin ci gaban jam’iyyar.

By Editor