*Ta musanta zargin da ake yi mata
Daga BASHIR ISAH
An gurfanar da Hafsat Surajo wadda aka fi sani da Chuchu, bisa zargin kashe abokin kasuwancinta, Nafiu Hafiz, a Kano.
Duk da dai da fari Hasfat ta yi ikirarin ita ce ta kashe marigayin, amma ta musanta zargin da ake yi mata yayin zaman sauraren shari’a da kotu ta yi a ranar Laraba.
An maka Hafsat a Kotun Chief Magistrate No. 37 ne da ke yankin Yankaba, Kano, inda ake zargin ta kashe Nafiu Hafiz.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa, ana zargin mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da wani Malam Adamu da aikata laifukan hadin baki wajen aikata babban laifi, boye laifi da kuma ba da bayanan karya ga ‘yan sanda.
Ya ce, “Idan jama’a za su iya tunawa, a ranar 21 ga Disamban 2023, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya ba da odar a tsare Hafsat Surajo, ‘yar shekara 24, kuma matar aure da ke zaune a Unguwa Uku Quarters, Kano, bisa zargin haddasa mutuwar Nafi’u Hafiz, mai shekara 38, biyo bayan rashin jituwa a gidansu.
“Haka nan, a sakamakon binciken ‘yan sanda an kama mijinta, Dayyabu Abdullahi, mai shekara 38 da wani Malam Adamu mai shekara 65, dukkansu a adireshi guda bisa zargin aikata laifuka kama daga yunkurin boye gaskiya da bada bayanan karya ga ‘yan sanda kan dalilin mutuwar.
“A yau, 27/12/23, kasancewar Hafsat Surajo babban abin zargi, ana zarginta da laifukan yunkurin kashe kantsa da kuma kisa wanda ka iya fuskantar hukuncin kisa.
“Yayin da ake zargin Dayyabu Abdullahi da Malam Adamu da laifin hadin baki wajen aikata babban laifi, boye gaskiya da kuma bada bayanan karya,” in ji jami’in.
