Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya rasu a safiyar Laraba bayan fama da rashin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa, Gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.
Marigayin ya bar duniya yana da shekara 67, bayan shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da kansar mafitsara.
Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan Gwamna Akeredolu ya rubuta wasikar tafiya neman lafiya, inda ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
Marigayin ya shafe kusan wata uku a kasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Nijeriya a watan Satumban da ya gabata.
