Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Kamar yadda mai ba da shawara na musamman kan siyasa ga shugaba Tinubu wato Alhaji Ibrahim Masari ya radawa shugaban suna Bala Tanimu Ashiru, ni kuma ga wasu matakan da shugaban ke Dauka ina son na yi ma sa kirari ne da zama DILA SARKIN WAYO don la’akari da yadda ya ke tinkarar lamuran Kasar tun lokacin da ya hau karaga a ranar 29 ga watan Mayu.
Dama ‘yan Nijeriya na cikin Kuncin tattalin arziki lokacin da ya hau karaga don haka cire tallafin man fetur da ya yi bai zama abun mamaki ba don dama ya yi alwashin yin hakan tun lokacin kamfen. Jama’ar kasa dai sun cigaba da daurewa tsadar kayan masarufi ne don kamar hakan ya zama jiki ne. Ba mamaki fahimtar yadda lamuran su ka cakude kuma ‘yan kasa cikin damuwa sai shugaban ya fito ya yi jawabi ya na nuna shi kan sa ya na jin irin wahalar da jama’a ke fama da ita don haka kamar ya na jajantawa da nuna zafin wuce nan gaba kadan. Da irin wannan jawabi sai sukan gwamnatin ya yi kasa tun da a baya ma ai an auka matsalar canjin kudi ta yadda ko mutum ya na da kudin ma ba zai iya amfani da su ba. Ga azabar hana yawo ta zamanin korona, ga kara kudin wutar lantarki, ga rufe kan iyakar kasa inda hakan ya fi yi wa mutan arewa illar da ba ta kwatantuwa.
Ga kuma haramta shigo da wasu kaya fiye da arba’in ciki har da shinkafa da ya kawo tsadar abinci duk da manoma na cikin gida sun amfana. Fitowa musamman da shugaban ya yi ya nuna kamar shi ma ya na shan wahala ya dan rage kaifin damuwar.
Wato magana ta rarrashi ta na da amfani maimakon a ji shiri kawai ko kuma in ma an yi maganar sai ta zama ba dadin ji ko ba tausayawa a ciki. Misali mutum ne ya zo neman taimako a wajen ka sai ya zama ba ka da abun taimakawar, a nan ba da hakuri ko kalmomi na tausayawa za su sa ko ba ka ba da komai ba mai bukatar zai tafi cikin kwanciyar rai kuma ya san da ka na da shi za ka ba shi, to amma in ka ce ma sa ko ka na da shi ba za ka ba shi ba don kudi ba abun banza ba ne to hakan ba zai taimaka ba. Ko kuma ka ma qi kula shi don shi talaka ne bai kai ka yi ma sa magana ba ko ma a ce maganar da ya yi ta bukata ta ba ka haushi don haka ka huce haushi a kan sa. Duk ba ma wannan shi ne babban abun da na ke son magana a kai ba.
Magana da na ke son yi ita ce kan yadda shugaba Tinubu kan yi amfani da hanyoyin warware takaddama ko da kuwa hakan don amfanin kan sa da jam’iyyar sa ne. Mu tuna yadda ya hada kan yankin Yarbawa ya maida shi karkashin jam’iyya daya.
Don haka ban yi mamakin masu cewa matakan da ya ke dauka ko abubuwan da ke faruwa a tsakanin nan yunkurin maida Nijeriya karkashin jam’iyya daya ne. Yanda Tinubu ya gudanar da tsari a lokacin ya na gwamnan Lagos shi ne ba lallai sai dan jihar Legas ba, ya kan iya dauko wanda ya ga ya dace daga sauran jihohin Yarbawa ya nada shi mukami a gwamnatin sa.
Irin wadannan mutanen na sa kan wayi gari sun zama masu fada a ji a jihohin su don haka sun zama wakilan yada manufofin sa. Da haka ya samu ya mamaye siyasar yankin kudu maso yamma ta yadda in mutum na son kuri’ar yankin sai ya zauna da shi sun yi yarjejeniya. Sauran yankuna ba su samu irin mai wannan tsarin ba in ka debe tsohon shugaba Buhari da mutan Arewa ke dauka na su ne musamman talakawa kafin daga bisani matsalolin da su ka nemi hallaka su gaba daya su ka sa su sauya tunani. Tambaya a nan waye ne zai iya fadawa ’yan Arewa ga wanda ya dace a zaba sai kawi su zabe shi?
Shin yau in tsohon shugaba Buhari ya marawa wani baya a zabe nan gaba zai iya lashe zaben ko zai samu kuri’ar ‘yan Arewa? Kafin samar da amsa sai mu duba yadda yankin mafiya yawan jama’a, kabilu da addini ke kasancewa in an samu wata fitina. Yaya jama’ar yankin su ka tinkari harin bom na jirgin soja marar matuki kan mutan Tudun Biri a jihar Kaduna?
wato abun takaici shi ne yankin ya zama yara ba sa girmama manya, manya ba sa jin tausayin yara. Rashin Tinubu a arewa ya sa ba a samun tasowar hamshakan ‘yan siyasa ko ‘yan kasuwa sai ma matasa su buge a kafafen sadarwar yanar gizo su na muhawara kan wacce ta iya kunu! wasu matasa mata da ya dace su na can makarantun koyon likitanci har ma tukin jiragen sama sai kawai su hau kafafen zamani su na ta zage-zage ko zunduma rawa da sakarci kuma ba wanda ya isa ya tsawata cewa hakan mummunan koma baya ne.
Mu koma kan darasin nan na yadda shugaba Tinubu ya zama Dila sarkin wayo kan muhimman matakai da ya dauka kan jihar Ondo da Ribas na tsawatawa da a baya ba haka a ke gani ba. Maimakon Tinubu ya ce ku ci kan ku sai ya zabi sa baki don warware takaddama don hakan zai amfani siyasar sa ko kuma hakan zai taimaki masu zaman ‘yan marina da juna.
Jihar Ondo mukarraban gwamna Rotimi Akredolu ne ke neman ture mataimakin gwamna Lucky Aiyedatiwa don basa son tasirin sa yayin da gwamnan ke ketare ya na jinya. Ribas kuma tsohon gwamna Nyesom Wike ke neman ture magajin sa wanda shi ya dora kan kujera gwamna Siminalayi Fubara don rashin yi ma sa biyayya kan muradun siyasa.
Kwamishina a jihar Ondo Razaq Obe ya yi zargin wasu na satar sa hannun gwamnan jihar Rotimi Akeredolu wajen amincewa da takardun da a ke turawa don sa hannun gwamna.
Obe ya baiyana haka ne a wasikar da ya turawa mataimakin gwamnatin jihar Lucky Aiyedatiwa don daukar matakin da ya dace kafin abun ya yawaita.
Kwamishinan ya hada da takarda da ya tura don neman amincewar gwamnan inda ya hada ta da wasu takardu ya ce ya gano akwai bambance-bambance.
Jinyar da gwamna Akeredolu ya ke yi ta sa ya gaza iya gudanar da aiki na tsawon wata 6 kuma duk da dawowar sa daga jinya a Jamus bai taka jihar ba.
Mukarraban gwamna jihar sun zargi mataimakin gwamnan da yi wa gwamnan zagon kasa har ta kai ga yunkurin tsige shi daga majalisar dokokin jihar.
In za a tuna shugaba Tinubu ya gayyaci masu ruwa da tsaki na siyasar APC a jihar inda ya sulhunta su da su daina dauki ba dadi.
Kakakin majalisar dokokin jihar Ribas Edison Ehie ya ayyana kujerun ‘yan majalisa 27 da su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC a matsayin ba kowa a kan su.
Ehie ya ayyana ‘yan majalisar da cewa sun sarayar da kujerun su a zaman da ya jagoranta a wani daki a gidan gwamnatin jihar lokacin da gwamna Siminalayi Fubara ya zo gabatar da kasafin kudi Naira biliyan 800.
Edison Ehie ya ce zai rubutawa hukumar zabe don sanar da ita wannan lamari don ta sake shirya zabe a mazabun ‘yan majalisar da su ka shige APC.
Gwamna Fubara ya marawa kakakin baya don a zahiri ya na taimaka ma sa wajen damvarwar da ke tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.
Ehie a yanzu dai na jagorantar majalisa mai mutum 4 ne kacal kuma kotu ta ba shi damar rike majalisar kafin yanke hukuncin karar da a ka shigar.
Zuwa yanzu kwamishinoni 3 a gwamnatin Fubara masu mara baya ga Wike sun yi murabus.
Cikin kwamishinonin har da na shari’a Zacchaeus Adangor.
Ganin wannan damvarwa ya sa shugaba Tinubu gaiyatar Wike da Fubara inda ya yi mu su sulhu da hana cigaba da rikicin. Tuni ma ’yan majalisa 25 da su ka sauya sheka daga PDP zuwa APC su ka janye barazanar tsige Fubara. Ko banza dama in ka zama shugaba zaman lafiya za ka so a duk sassan kasar ka.
Kuma ba ma sai Tinubu ya tilasta nada gwamna dan APC a Ribas ne zai samu goyon baya a alamun burin tazarce a 2027 ba don ai Wike ya na PDP ya riqa yi wa jam’iyyar zagon kasa har ya ma ta babbar illa a zaben shugaban kasa kuma har yanzu ba ta farfado daga dambarwar ba.
Kammalawa;
Shugaba Tinubu Dila Sarkin wayo zai cigaba da irin wadannan dabaru na nazartar wanda zai taimake shi ko ba jam’iyyar su daya ba. Duk mai son gano sirrin Tinubu sai ya bi salon yadda ya mulki Lagos har ya maida yankin kudu maso yamma mai bin jam’iyya daya.
Shin ta alheri ne za a samu nasara shin ta ganawa kai tsaye kamar yadda Tinubu ya yi da ‘yan kungiyar kwadago ne; ta haka a ke cimma nasara ko ba dadi kuma b aba amincewar jama’a a mulki kasa a gama ko ba yabo ya zama ba fallasa.
