Ba zan iya cewa ga mutum ɗaya da ya shigo da ni harkar fim ba – Hajara Yusuf Makama 

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Idan Allah ya kaimu ranar 26 ga Disamban nan za a nuna Fim din Pricenss Of Galma na kamfanin Jammaje Production a katafaren dakin taro na Musa Abdullahi da ke harabar sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano wanda ake sa ran dubun dubatar mutane za su halarta domin kallon wannan fim din da ya zamo zakaran gwajin dafi a cikin finafinan Kannywood.

Jarumar Kannywood Hajara Yusuf Makama na daya daga cikin jarumai masu tasowa da a ke ganin zuwa nan gaba kadan za ta kai matakin manyan jaruman da ake ji da su a Kannywood, ita ce jarumar da ta ja wannan fim din a matsayin Gimbiya.

Ta dalilin haka ne wakilin Blueprint Manhaja a Kano, ya samu tattaunawa da ita a game da irin rawar da ta taka a fim din da kuma batutuwa da suka shafi shigowar ta masana’antarKannywood. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

HAJARA MAKAMA: Ni dai sunana Hajara Yusuf Makama, kuma an haife ni a garin Kaduna a shekarar 1997, amma dai asalin iyayena ‘yan Maiduguri ne kuma ni Kanuri ce daga Karamar Hukumar Bama. Na yi karatu tun daga firamare har matakin NDE, yayin da yanzu haka Ina HND.

Da yake har yanzu kina matakin karatu ne, ko ya aka yi ki ka samu kanki a cikin harkar fim?

Gaskiya na daxe a harkar don tun Ina matakin sakandare nake yin fim, to amma da na fara NDE cina sai na dakatar, saboda ba zan iya hada karatu da fim ba a lokacin don haka sai na dan ja baya sai yanzu da na gama sai na dawo saboda a yanzu da nake HND karatun ya fi mini sauqi sosai.

Kin ce kin dade da fara fim, ko za ki fada mana fim din ki na farko da ki ka fara?

Gaskiya ba zan iya cewa ga fim din da na fara yi ba, don na manta amma dai cikin finafinan da na yi zan iya tunawa akwai ‘Karamin Sani’, ‘Telan Mata’, ‘Kawayen Amarya’, ‘Hauwa Kulu’. Kai suna da yawa dai ba zan iya kawo su dukka ba.

Tun a farko ma waye ya yi silar shigar ki harkar fim?

To fa! Gaskiya kai tsaye ba zan iya cewa ga wani mutum daya da ya zama shi ne silar shiga ta harkar fim ba, sai dai na ce daman tun can Ina da sha’awar yin harkar, to a unguwar mu akwai wani da na sani a lokacin kamar wasa ya kira ni lokacin waka ce ma za su yi ya kira ni na je muka yi bidiyon wakar, tun Ina irin dardar din nan yana karfafa min gwiwa da cewar idan na saka a zuciya ta zan iya to zan yi nasara. To a haka na fara a wancan lokacin.

A yanzu masu kallo da wanne fim suka fi sanin ki da shi?

To Ina ganin dai fim din da aka fi sani na da shi shi ne, ‘Telan Mata’, sai kuma fim din ‘Kawayen Amarya’, wadannan su ne duk inda na je zan ji ana cewa an ganni a cikin su, sai kuma fim din ‘Ana Barin Halak’, shi ma mutane suna yin maganar sun ganni a cikin sa.

A yanzu kuma kin samu kanki a cikin wani sabon aiki wanda yake shi kuma ba fim din Hausa ba ne. Shin ko daman kin taba yin fim na Turanci?

E gaskiya na yi finafinai na Turanci a baya. Amma wannan aikin na ‘Princess Of Galma’ ya bambanta da sauran ta fuskoki da dama domin ka ga dai shi wannan duk da na Turanci ne to amma labarin Bahaushen labari ne don haka sai nake ganin wannan ya fi dacewa da ni saboda a wannan an nuna tsantsar al’adun Kasar Hausa ne, da kuma wayar da kan mutane yadda masarautunmu na Arewa suke.

Sannan kuma a wannan fim din sai ya zama ni ce jarumar don haka an ba ni matsayi mai girma a fim din kuma gaskiya na dauki fim din ‘Princess Of Galma’ da muhimmanci shi ya sa na fi mayar da hankali na a kan aikin sa don na ga na bayar da abin da ake so yadda kowa zai ji dadin kallon aikin kuma ba zan iya kwatanta jin dadin da na yi ba da aka sanar da ni ni ce zan fito a matsayin jarumar ‘Princess Of Galma’ domin na san fim din zai daga daraja ta don haka na ji dadi da aka ba ni damar da ba kowa ya samu ba, Ina godiya sosai ga Malam Kabiru Musa Jammaje da ya jawo ni ya dora ni a wannan babban rol din wadda na fito a matsayin ‘yar sarki.

Wanne kira za ki yi ga masu gudanar da harkar fim a matsayin ki na jaruma mai tasowa?

Ni kiran da zan yi shi ne, a ci gaba da taimakon masu tasowa da suke da zuciyar yin aikin da gaske don Allah a rinqa ba su dama kamar yadda na samu dama a wannan fim din ‘Princess Of Galma’ ta haka ne mu ma za a san irin namu kwazon a cikin harkar fim, kuma mu samu damar bayar da tamu gudunmawar da ta dace.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By Editor