Daga BASHIR ISAH
A halin da ake ciki, an rantsar da Mukaddashin Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin sabon gwamnan jihar.
A ranar Laraba da misalin karfe 5:20 na yamma aka rantsar da sabon Gwamnan wanda Babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Olusegun Odusola ya jagoranta.
Rantsar da Aiyedatiwa a matsayin sabon Gwamnan Ondo ya biyo bayan rasuwar Gwamnan Jihar ne, Rotimi Akeredolu, wanda Allah Ya yi wa cikawa ranar Laraba a wani asibitin Jamus.
Rantsarwar ta yi daidai da tanadin Kundin Tsarin Mulki na kasa na 1999 (wanda aka gyara) gudun kada a bar wani gibi a shugabancin jihar.
Sashe na 191(1) na Kundin ya ce, “Mataimakin Gwamna ya rike ofishin gwamna a duk lokacin da ofishin ya kasance babu kowa a sanadiyar mutuwa, ko murabus, ko tsigewa, ko kuma dai wani dalili ya sanya aka cire gwamnan daidai da sassa na 188 ko 189 na wannan Kundi.”
