Babaji

5689 Posts

Kamala Harris ta yi tir da matakin Trump na yaƙar Iran, ta yi gargaɗin ɓarkewar yaƙi tsakanin ƙasashe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris, ta yi kakkausar suka game da hare-haren soji da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta bada umarnin kai wa Iran. Ta bayyana matakin a matsayin ganganci da ka iya jefa Amurka cikin yaƙin da ba za ta so sakamakonsa ba. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Kamala Harris ta ce hare-haren wani hatsarin ƙara tsananta rikici ne, wanda ke jefa rayukan sojojin Amurka cikin haɗari tare da tada zaune tsaye a yankin da kuma rage amincewar Duniya ga jagorancin Amurka. Harris ta bayyana matakin sojin na…
Read More

Iran na duba yiwuwar janyewa a Gasar Kofin Duniya na 2026 kan yaƙi da Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙasar Iran na duba yiwuwar ficewa daga gasar cin kofin duniya na 2026 a hukumance. Hakan na nufin tawagar 'yan wasanta ba za su je ƙasar Amurka ba domin fafatawa a wasannin gasar ba na wannan shekarar. A sabon jaddawalin wasannin, Iran na da uku na rukuni da za ta yi da wasu ƙasashe a Amurka. Iran ta yi imanin cewa rayuwa ba za a iya kwatanta ta da ƙwallon ƙafa ba kuma ba za ta ɗauki haɗarin zuwa gasar cin kofin duniya ba. A halin yanzu an shiga kwana na biyu ana fafata…
Read More

Yaƙin Iran da Amurka/Isra’ila: Gwamnatin Tarayya ta shawarci ‘yan Nijeriya da ke ƙasashen Gabas ta Tsakiya su kula

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta shawarci ’yan Nijeriya mazauna Gabas ta Tsakiya musamman ma Iran da ƙasashen yankin Gulf, da su ƙara ɗaukar matakan tsaro sakamakon tashin hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a ranar Asabar, gwamnati ta ce tana sa ido kan rahotannin hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wasu wurare a Iran, da kuma martanin Iran da ya shafi sassan yankin Gulf. Hukumomi sun buƙaci ’yan Nijeriyar da su kasance a faɗake, su guji wuraren da ake kai wa hari kamar sansanonin soji da gine-ginen…
Read More

Zamfara: Gwamna Lawal ya jagoranci taron gaggawa akan tsaro, ya jajenta wa waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jajenta wa mutanen da hare-haren ’yan bindiga suka shafa a sassa daban-daban na jihar, yana mai tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar yankin. A ranar Juma’a gwamnan ya kira tare da jagorantar wani taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jihar a ɗakin taro na Gidan Gwamnati da ke Gusau. Taron ya haɗa shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin duba halin da ake ciki da kuma ɗaukar matakan gaggawa. A sanarwar da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala…
Read More

Iran ta tabbatar da rasuwar Jagoran Musuluncin ƙasar a harin Amurka da Isra’ila

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Iran da kafar yaɗa labaran ƙasar sun tabbatar da mutuwar Jagoran Musuluncin ƙasar, Ali Khamenei bayan ruwan wuta da Amurka da Isra'ila suak ƙaddamar a ranar Asabar, lamarin da ya yi sanadin faɗaɗa rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da sanya alamar tambaya game da makomar ƙasar. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan ikirarin farko da shugaba Donald Trump ya yi na kisan jagoran addinin a hare-haren da suka kai a sassan ƙasar. A sanarwar kafar yada labaran, ba a bayyana yadda aka kashe jagoran addinin, mai shekaru 86 ba da kuma wanda…
Read More

Sufeto Janar Disu ya cire ACP Bukola Kuti a PSO, ya mayar da ita NIPSS Kuru

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sufeto Janar na Rundunar 'yan sanda na riƙo, Olatunji Disu ya tsige ACP Bukola Kuti a muƙamin Babbar Jami'a mai daraja ta 2 (PSO2) ta jami'ai a lokacin tsohon Sufeto Janar Kayode Egbetokun, inda ya mayar da ita Cibiyar Nazarin Tsare-tsare da Dabaru ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru. Majiyoyi da dama daga rundunar sun tabbatar wa jaridar ShaharaReporters cewa sauyin zai fara aiki ne a nan take, wanda ya haddasa cece-kuce acikin manyan jami’an 'yan sanda musamman bisa la'akari da makomar matsayinsu. ACP Kuti ta yi aiki ne a matsayin PSO2 ga Egbetokun,…
Read More

Tinubu ya sake naɗa Abubakar Audi a Kwamanda Janar na Cibil Defense

Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗa Dakta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Kwamanda-Janar na Hukumar Tsaron al'umma ta Cibil Defense (NSCDC) na wani sabon wa’adin shekaru biyar. Sabon naɗin ya fara aiki ne q ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu, 2026 . An fara naɗa Dakta Audi a wannan matsayi ne a shekarar 2021 ta hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Wa’adinsa na farko na shekaru biyar ya ƙare ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake halartar bikin Ranar Kariya ta Duniya ta 2026 a hedikwatar NSCDC ta ƙasa da ke Abuja. Litinin mai zuwa ake sa ran…
Read More

Iran ta yi ruwan wuta akan sojin Amurka da ke Ƙatar, Bahrain da wasu ƙasashe

Rahotanni sun nuna cewa ƙasar Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya akan sansanonin sojojin Amurka da ke wasu ƙasashen yankin gabas ta tsakiya. Hakan na nufin mayar da martani ga hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai mata da safiyar yau Asabar. Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila, IDF ta fitar, ta tabbatar da gano makamai masu linzami da Iran ta harba cikin Isra'ila, amma tana ƙoƙarin ganin ta kakkaɓo su. Haka ma Qatar ta tabbatar da cewa Iran ta kai hari kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke ƙasaer, kodayake ta ce an kakkaɓo hare-haren. Ita ma…
Read More

Trump ya kirayi ‘yan Iran su kifar da gwamnatin Musuluncin ƙasar

Shugaba Donald Trump na Amurka ya buƙaci Iraniyawa su yi amfani da manyan hare-haren Amurka da Isra'ila wajen kifar da gwamnatin ƙasar. A cikin wani jawabi da ya yi ta bidiyo, Mista Trump ya ce ''Idan muka gama namu, ku kuma ku ƙwace gwamnatin, taku ce, ina ganin wannan ce damar da kuka samu ta yin hakan''. Ya kuma faɗa wa dakarun sojin Iran cewa za a ba su ''kariya'' idan suka amince su ajiya makamansu, ko kuma su ''fuskanci mutuwa''. A farkon watan Janairu ne Trump ya yi barazanar kai harin bom kan Iran saboda yadda jami'an tsaron ƙasar…
Read More

‘Yan bindiga sun mamaye wuraren da babu shugabanci a Bauchi, inji Gwamna Bala bayan ganawa da Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Juma'a Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwa game da faɗaɗar ayyukan 'yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Alƙaleri da ke Jihar Bauchi, inda ya yi gargaɗin cewa matakin da al'amarin yake a yanzu ka iya haddasa babbar fitina matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa a kai ba. Bala Mohammed ya bayyana haka ne bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya bai wa shugaban ƙasar ba'asin halin tsaro a sassan jihar tasa. Da yake jawabi ga manema labarai, Ƙauran na Bauchi ya ce 'yan bindigar sun fara ƙarfi a…
Read More