Babaji

5689 Posts

Kotu ta tabbatar babban taron PDP na Ibadan, ta amince da jagorancin tsagin Turaki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Jihar Oyo ta tabbatar da sahihancin babban taron Jam’iyyar PDP da aka yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025 a Ibadan, inda aka zaɓi sabon shugabancin Jam’iyyar. Alƙalin kotun, Mai Shari'a Ladiran Akintola, ya ce taron da zaɓukan sun cika dukkan sharuɗɗa da ka’idojin da dokokin ƙasa da na jam'iyyar suka tanada. Kotun ta kuma ƙaryata dukkan buƙatun da wasu suka gabatar waɗanda ke ƙalubalantar taron, ciki har da neman dakatar da sakamakon taron, inda ta ce ba su da tushe. Hukuncin ya umurci INEC da ta amince da…
Read More

Kaduna: Gobara ta tashi a fadar Sarkin Jama’a

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Juma'a ne gobara ta ƙone wani sashi na fadar sarki a Kafanchan, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Jama'a da ke Jihar Kaduna, lamarin da ya jafe al'ummar yankin cikin firgici. Gobara ta ƙone sashin fadar ne,wadda mai martaba sarkin Jama'a, Alhaji Dokta Muhammad Isa Muhammad ke jagoranta. Rahotanni da hotuna sun tabbatar da cewa gobarar ta kama ne da yamma, inda jama'a suka kai ɗauki domin kashe ta. Saidai jami'an tsaro sun hana cincirindon mutanen da suka yi niyyar ƙarasawa saboda halin rashin tabbas, da kuma bai wa ƙwararrun masu kashe gobara damar yin…
Read More

Isra’ila ta ƙaddamar da hari kan Iran

Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-haren soji akan Iran, inda Shugaban Amurka, ya tabbatar da cewa an fara manyan ayyukan fada a yankin. Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren ramuwar gayya, lamarin da ya kara dagula yanayin tsaro a Gabas ta Tsakiya. Hotuna da bidiyo da ke yawo sun nuna hayaki na tashi a sararin samaniyar birnin Iran, yayin da aka ji karar fashe-fashe a birane biyar na Iran. Shugaba Trump ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su “kwace mulkin kasarsu,” yana mai cewa wannan na iya…
Read More

Tallafin sojojin Amurka bai rage darajar Nijeriya ba – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta ce tallafin sojoji da gwamnatin Amurka ta kawo wa ƙasar ya samu ne ba tare da biyan wani farashi ba, sannan hakan bai rage darajar Nijeriya ba ko ta wace hanya. Da yake ganawa da manema labarai a Abuja game da ayyukan dakarun a ranar Juma'a, Kakakin babban ofishin tsaron, Manjo Janar Michael Onoja ya ce tallafin na Amurka ya samu ne domin bai wa sojojin ƙarin ƙarin horo da ƙarfafa wa ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta'addanci, yana mai cewa hakan ba abu ne da za a riƙa yi…
Read More

Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara bakwai ga Sanata Bassey kan badaƙalar miliyan N240

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ƙolin Nijeriya ta jaddada hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ga Sanata Albaert Bassey bisa hannu a badaƙalar miliyan N240. A wani zama na tawagar alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Stephen Jonah Adah, kotun ta tabbatar da hukuncin, wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a baya bisa samun sa da hannu a laifin. Haka kuma kotun ta umarci a dawo da kuɗaɗen waɗanda adadinsu ya kai jimillar Naira miliyan 204 ga gwamnatin Jihar Akwa-Ibom. A cewar Kotun Ƙolin, yayin da ta Ɗaukaka Ƙarar ta yanke hukuncin, ba ta bayyana ko za…
Read More

Sojoji sun halaka ‘yan ta’adda 312, sun ceto mutanen 409 a Fabarairu, inji Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun da ta baza domin ƙaddamar da muhimman atisaye daban-daban a sassan ƙasar sun yi nasarar kama mutane 312 bisa zargin su da hannu a laifukan ta'addanci, sannan sun kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su guda 409 a watan Fabarairu. Haka kuma, ta ce aƙalla mayaƙan 'yan ta'adda guda 46 tare da iyalansu ne suka miƙa wuya. Da yake zantawa da manema labarai akan ayyukan sojoji ranar Juma'a a Abuja, Daraktan harkokin yaɗa labaran DHQ, Manjo-Janar Michael Onoja ya ce sojojin sun kuma…
Read More

Ina danasanin kasancewa cikin waɗanda suka tallata APC har ta samu mulkin Nijeriya – Atiku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a jamm'iyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar ya bayyana nadamarsa akan kasancewa cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC a shekarar 2014 domin kayar da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan. Atiku ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai da jagororin adawa suka shirya a Abuja, ranar Alhamis. A cewarsa, dalilin haɗuwar manyan ’yan siyasa a wancan lokaci shine samar da sauyi a shugabanci da inganta rayuwar al’umma. Saidai ya yi ikirarin cewa halin da ƙasar ke ciki a yanzu ya fi muni a ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Atiku shaguɓe kan komawar Fintiri APC

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar shaguɓe bayan sauya sheƙar Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri zuwa jam’iyyar APC, tana mai cewa matakin babbar koma-baya ne ga burinsa na takarar shugaban ƙasa. Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X a yau Juma’a, inda ya ce sauya sheƙar Fintiri na nuna cewa Atiku ba shi da cikakken farin jini a jiharsa ta asali. Sanarwa ya ƙara da cewa "gwamna Finitri ya ɗauke wa Atiku duk wata ƙarfinsa ta jiharsa zuwa jam’iyyar shugaba Bola Tinubu…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta karɓi ikon mallakar filin wasa na Ahmadu Bello

Jihar Kaduna na daf da buɗe sabon babi a tarihin bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi bayan da Gwamna Uba Sani ya rattaɓa hannu akan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) wadda ta tabbatar da sauya mallaka da miƙa Filin Wasan Ahmadu Bello daga Gwamnatin Tarayya zuwa Gwamnatin Jihar Kaduna.‎An cimma wannan matsaya ne bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Gwamna Uba Sani ya sanya hannu a madadin Jihar Kaduna, yayin da Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Alhaji Shehu Dikko, ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya.‎Shugabannin Hukumar Wasanni ta Ƙasa sun yaba wa gwamnatin Kaduna bisa namijin kokarin da…
Read More

An fitar da jaddawalin ‘yan 16 na Kofin Zakarun Turai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da aka kammala zagayen wasannin cike gurbi a gasar zakaran nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na 2025/2026, Hukumar UEFA ta shirya ƙungiyoyin da za su kara da juna a rukunin 'yan 16. Hakan na zuwa ne ƙasa da watanni uku da za a ƙarƙare gasar, wadda ƙungiyar PSG ta lashe a kakar wasan da ta gabata. Ga jaddawalin yaɗa wasannin suke kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito: Real Madrid vs Manchester City Bodø/Glimt vs Sporting PSG vs Chelsea Newcastle vs Barcelona Galatasaray vs Liverpool Atletico Madrid vs Tottenham Atalanta vs Bayern Munich Bayer…
Read More