Babaji

5689 Posts

Badaƙalar N8.7bn: Kotu ta janye belin Malami da iyalinsa, ta tura su kurkukun Kuje da Suleja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi hukuncin sabunta shari'ar tsohon Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na Ƙasa (AGF), Abubakar Malami bayan da ta yanke cewa ta koma sabuwa. Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta ce tunda an sake gabatar da shari'ar a gaban kotun a matsayin sabuwa, dukkan hukuncin da aka yi baya har da belin da Alƙali Emeka Nwite ya bayar, an soke su. Wannan hukunci ya nuna cewa wajibi ne tsohon ministan ya shigar da sabon ƙorafin neman beli kafin kotun ta duba yiwuwar amince wa sako shi da iyalansa. Hukumar…
Read More

Noman rani: Gwamna Lawal ya Raba kayan noma ga manoma a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon takin zamani da wasu muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a kakar noman rani a faɗin jihar. An ƙaddamar da shirin ne a ranar Alhamis a cibiyar Fadama III da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Noma ta jihar a Gusau. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, kayayyakin da aka raba suna da matuƙar muhimmanci wajen ƙara yawan amfanin gona, rage asarar da ake yi bayan girbi, da kuma bunƙasa noma mai ɗorewa. Kayayyakin da aka raba sun haɗa…
Read More

An tasa ƙeyar tsohon shugaban NNPC zuwa kurkuku a Amurka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata kotun gunduma da ke Amurka, ta yanke wa tsohon babban jami'i a Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Paulinus Okoronkwo hukuncin ɗaurin watanni 87 a gidan yarin tarayya bisa samun sa da hannun a laifin karɓar cin hancin Dala miliyan 2.1 da aka danganta da wani kamfanin mai na ƙasa-da-ƙasa. Okoronkwo, wanda a baya shi ne janar manaja na sashen samar da albarkatun mai na NNPC, an same shi ne da laifuka da dama da suka haɗa da sauya akalar kuɗaɗen ƙasa, ƙaurace wa biyan haraji da gangan da kuma ƙoƙarin hana…
Read More

Babu ikon da ya isa hana Musulmi aiki da Shari’ah, inji Majalisar Ƙolin Musulunci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Ƙolin Shari'a a Nijeriya (SCSN) ta ce babu wani iko ko ƙarfin mulki da zai hana Musulmi aiki da Shari'ah a ƙasar. Sakataren Majalisar, Nafi'u Baba Ahmad ya bayyana haka a wata takarda yayin da yake tsokaci game da rahoton da kwamitin majalisar dokokin Amurka ya miƙa wa Shugaba Donald Trump a kwanan nan. Hakan na zuwa ne bayan da mambobin kwamitin, wato Ɗan majalisa Riley Moore da Chris Smith suka kammala bincike akan zargin kisa kiyashi ga al'ummar Kirista a Nijeriya. A rahoton nasu, sun bayyana dokokin shari'a da ɓatanci a matsayin…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi ‘yan adawa da ruɗar da jama’a akan gyare-gyaren dokar zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki jam'iyyun adawa musamman ADC da NNPP, inda ta zarge su da yaɗa kuskure da ƙoƙarin haddasa abin da zai janyo cece-kuce acikin al'umma game da dokar zaɓe da aka yi wa kwaskwarima a kwanan nan. A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a jiya Alhamis, fadar ta yi watsi da zarge-zargen da 'yan adawar suka yi a wani taron manema labarai a Abuja, inda suka soki Shugaba Bola Tinubu da Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin APC. Ya bayyana ikirarin nasu a matsayin kalaman "ƙarya masu…
Read More

Kano: Hukumar Yaƙi da Rashawa ta tilasta wa ɗan Kwankwaso da wasu tsoffin kwamishinoni dawo da motocin gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Al'umma da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano ta ƙwato motoci biyar na gwamnati daga hannun wasu tsofaffin kwamishinoni da suka yi murabus daga majalisar zartarwar jihar. Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ya ce an ɗauki matakin ne bayan sun ƙi mayar da kadarorin gwamnati duk da gargadi da aka yi musu, inda aka samu umarnin kotu kafin aiwatar da aikin. Ya bayyana cewa biyu daga cikin motocin su ne ainihin waɗanda gwamnati ta saya, yayin da bincike ya nuna an sayar da sauran, aka maye gurbinsu da wasu motoci. Hukumar ta…
Read More

El-Rufa’i ya nemi kotu ta haramta wa ICPC, EFCC da SSS rufe asusun bankunansa da ƙwace kadarorinsa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta neman a hana hukumomin ICPC, EFCC, DSS da kuma Antoni Janar na Ƙasa (AGF) ɗaukar matakin rufe masa asusunsa na banki ko ƙwace kadarorinsa. A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026 da lauyansa Oluwole Iyamu (SAN) ya shigar, El-Rufai ya nemi kotu ta bada umarnin wucin-gadi domin hana su aiwatar da komai har sai an kammala sauraron shari'arsa. Ya kuma buƙaci kotun da ta tabbatar da cewa kuɗin fansho da alawus-alawus din barin aiki da ya karɓa bayan kammala wa’adinsa daga…
Read More

INEC ta fitar da sabon jaddawalin zaɓen 2027, za a yi na shugaban ƙasa a 16 ga Junairu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar da sabon jaddawalin tsare-tsaren babban zaɓen 2027, inda ta sauya lokutan gudanar na shugaban ƙasa da gwamnoni kamar yadda hukuncin dokar zaɓe ta 2026 ya tanada. INEC ta sanar da cewa, a yanzu za a yi na shugaban ƙasa da 'yan majalisar dokokin ƙasa a ranar Asabar, 16 ga watan Junairu, 2027, yayin na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi za su gudana a 6 ga Fabrairu, 2027. Hakan na zuwa ne bayan kwaskwarima ga Dokar Zaɓe ta 2022 da gabatar da sababbin tsare-tsaren lokuta a ƙarƙashin…
Read More

‘Ba ni da bindiga’: Tinubu kan zargin sa da kassara ɓangaren adawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da ikirarin cewa gwamnatinsa tana ƙoƙarin kassara jam'iyyun adawa, yana mai cewa ba yi amfani da ikon mulki ba wajen tursasawa wajen barin jam'iyya ga 'yan siyasa ko rufe bakin 'yan adawa. Tinubu ya bayyana haka ne a yayin liyafar buɗe baki na musulmi da kirista da ya ƙunshi sanatoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shugaban ƙasar ya yi tsokacin ne a lokacin yake bada amsa game da sukar Jam'iyya mai mulki (APC) akan ƙara ƙarfi da hanyar zargin tursasawa 'yan adawa komawa cikinta. "Lallai ne…
Read More

Yanzu-yanzu: Atiku, Obi, Amaechi, Mark da wasu jagororin adawa sun yi watsi da Sabuwar Dokar Zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyun adawa a Nijeriya, sun yi watsi da sabuwar dokar zaɓe ta 2026 da aka yi wa gyaran fuska a kwanan nan da majalisar dokokin ƙasar da tabbatar kuma Shugaba Bola Tinubu ya amince da ita a hukumance. Sun yi kira ga majalisar dokokin da ta gaggauta shirin sake sabon gyara akan kundin dokar tare da cire dukkan hukunce-hukuncen da suka janyo cece-kuce acikin al'umma. Jam'iyyun sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka yi wa laƙabi da 'kiran gaggawa don ceto dimukraɗiyyar Nijeriya" da kaz yi a otal ɗin Transcorp…
Read More