26
Feb
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Majalisar Dattawa akan Kuɗaɗe, ya bayar da izinin kama babban rajistiran Hukumar kula da Lamuran Rajistar Harkokin Kasuwanci (CAC), Hussaini Ishaq Magaji bisa zargin sa da ƙin amsa gayyatar da majalisar da sha yi masa a baya. Kwamitin ya bada izinin ne a ranar Alhamis yayin zama akan kare kasafi da ya ƙunshi Ma'aikatar Kuɗi da hukumomin da ke ƙarƙashinta. Shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa ya zargi Ishaq Magaji da ƙin biyayya ga kwamitin da gangan. Ya ce, ana gayyatar sa ne domin ya zo ya fayyace matsalolin da suka shafi lamuran kuɗaɗe…
