02
Mar
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani jirgin yaƙin Amurka ƙirar F-15E ya yi hatsari a Kuwait yayin farmakin Iran a sansanin sojon saman Amurka, kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna. Al'amarin ya faru ne a tsawon mil shuda daga sansanin Ali Al Salem. An ga yadda jirgin ya ƙwace tare da nufin ƙasa a lokacin da yake ci da wuta ta ƙarƙashinsa. Aƙalla ɗaya daga cikin matuƙa jirgin ya yi nasarar fita daga ciki ba tare da samun wani rauni ba, wanda ya samu agajin daga mazauna yankin. Saidai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken…
