03
Mar
Wasu sabbin bayanai sun bayyana a game da kamawa da tsare Maryam Bukar, wadda ake zargin ta taɓa yin alaƙar soyayya da shugaban Bola Tinubu. Majiyoyi sun shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa an tsare Maryam Bukar a wani sansanin soja na tsawon watanni takwas ba tare da damar ganin lauyoyi ko iyalanta ba, inda ake zargin hakan ya faru ne bisa umarnin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. A ranar 19 ga Fabrairu, wani rahoto da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta wallafa ya zargi Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da tsare matar…
