04
Mar
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa (NERC) ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su biya Naira biliyan 20.33 da ake bin su na kuɗaɗen mita ga kwastomomi cikin shekara guda. Za a dawo da kuɗaɗen ne, waɗanda ta ce lissafi su zai fara ne tun daga ranar 1 ga watan Maris, 2026. Wannan kuɗi ya shafi tsarin samar da mita na masu zaman kansu (Meter Asset Provider MAP), inda kwastomomi suka biya kuɗin sayen mita da kansu, domin a mayar musu da kuɗin daga baya. Hukumar ta bayar da wannan…
