Babaji

5689 Posts

‘Yan bindiga sun farmaki motocin Amaechi a Ribas, sun ƙone ofishin ADC

Wasu 'yan bindiga a Jihar Ribas, sun kai hari akan tawagar tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun ƙone ofishin jam’iyyar adawa ta ADC a yankin. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Ikwerre a yau Juma’a, yayin da Amaechi ke kan hanyarsa ta zuwa garinsu na Ubima domin yin rajistar shiga jam’iyyar ADC ta hanyar tsarin e-registration. Gabanin isowarsa, wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun tare hanyoyi tare da hana wasu magoya bayan jam’iyyar ADC shiga garin domin halartar taron rajistar. Rahotanni sun ce, a daren…
Read More

Tinubu ya bayyana ƙasashen da ya aike da sababbin jakadun Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmud Yakubu, a matsayin jakadan Nijeriya a kasar Ƙatar. Haka kuma shugaban kasar ya tura tsohon minista, Femi Fani-Kayode, a matsayin jakadan Nijeriya a Jamus, yayin da ya nada Aminu Dalhatu jakadan Nijeriya a Birtaniya. Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma'a. Rahotanni sun nuna cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta riga ta tabbatar da sunayen jakadun tun a watan Disambar da ya gabata, kafin daga bisani shugaban kasar…
Read More

Kotu ta bada belin Malami da iyalinsa akan N200m kowanne

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada belin Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na ƙasa (AGF), matarsa Asabe Bashir da kuma ɗansa Abdulaziz Malami. Mai shari'a Joyce Abdulmalik je ta yi hukuncin a yau Juma'a inda ta yanke cewa kowane ɗaya daga cikinsu zai biya Naira miliyan 200 da kuma mutane biyu da za su iya tsaya masu aka belin. Haka kuma, kotun ta buƙaci da su bada fasfo ɗinsu a ajiye shi a gaban ƙuliya har zuwa lokacin kammala shari'ar. Ga yadda sharuddan belin nasu yake dalladalla: Kowanne zai bada beli na ₦200,000,000…
Read More

Majalisar Dattawa ta gayyaci tsohon Shugaban NNPC, Kyari da wasu kan zargin ɓatar tiriliyan N210

Majalisar Dattawa ta gayyaci tsohon Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Mele Kyari, domin amsa tambayoyi kan zargin kashe Naira tiriliyan 210 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023 da aka ce babu cikakken bayani game da rahoton binciken kuɗi a kai. Haka kuma majalisar ta nemi tsohon shugaban kula da harkokin kuɗi a NNPCL, Umar Isa da kuma tsohon shugaban gudanarwa na NAPIMS, Bala Wunti su gurfana a gaban ta. Kwamitin majalisar ya yi barazanar fitar da takardar kamu wato (warrant of arrest) idan ba su halarci zaman da za a gayyace su ba. Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada…
Read More

Trump ya ba Iran sharaɗin zaɓar magajin Ali Hosseini Khamenei

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa wajibi ne Amurka ta taka rawa wajen zaɓen sabon jagoran ƙasar Iran bayan rasuwar jagoran addini na ƙasar, Ali Khamenei. Trump ya kuma yi watsi da yiwuwar ɗan Khamenei, Mojtaba Khamenei, ya gaji kujerar jagorancin ƙasar, inda ya bayyana shi a matsayin wanda “ba za a amince da shi ba, kamar yadda ya shaida wa Axios a wata hira. A cewarsa, Amurka na son ganin an samu sabon shugaba a Iran wanda zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da rage tashin…
Read More

El-Rufa’i ya nemi ICPC ta biya tarar biliyan N15.6 kan kamawa da zargin ɓata masa suna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da iyalansa sun nemi Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC), shugabanta da wasu mambobin hukumar da su biya shi diyyar Naira biliyan 15.6 bisa kamawa da tsare shi da kuma zargin yin wasu kalaman ɓatanci akansa. Hakan na ƙunshe ne a wata takardar ƙorafi dake ɗauke da 4 ga Maris 2026, wadda ta fito daga lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Ubong Akpan, kuma an kai ta hedikwatar hukumar ICPC da ke Abuja. Rahotanni sun nuna cewa El-Rufai na hannun ICPC tun bayan da EFCC ta bayar da belinsa a ranar…
Read More

Kofin duniya na 2026: Super Eagles ta ɗebe tsammani bayan FIFA ta tabbatar da DR Congo a gasar

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta ce ƙasar DR Congo ce za ta wakilci Afrika a wasannin cike gurbi domin shiga gasar Kofin Duniya na 2026, yayin da Super Eagles ta Nijeriya rasa damar. Matakin da ya kawo ƙarshen burin Super Eagles ta Nijeriya na zuwa gasar kai tsaye. An shirya gasar tantancewar daga ranar 26–31 Maris 2026 a biranen Guadalajara da Monterrey, na ƙasar Mexico, inda ƙungiyoyi shida za su fafata don samun guraben ƙarshe biyu na gasar cin kofin gasar duniya. Ƙungiyar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta gabatar da ƙorafi, tana ikirarin cewa DR Congo ta…
Read More

Tinubu ya dakatar da tsarin biya ta na’ura a filayen jiragen sama na tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta dakatar da tsarin biyan kuɗaɗe ta na'ura a filayen jiragen sama na Gwamnatin Tarayya. Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya sanar da haka a yau Laraba bayan zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka gudanar da Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja. Ya ce, Shugaban ƙasar ya kuma umarci a gaggauta dawo da tsarin da zai taimaka wajen inganta tsarin ta yadda al'umma da dama za su amfana. A ranar 1 ga watan Maris ɗin shekarar nan ta 2026 ne Hukumar Kula da Filayen…
Read More

Hon. Haruna Doguwa ya zama shugaban APC a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya zama sabon Shugaban jam’iyya mai mulki (APC) a Jihar Kano. An gudanar da zaɓensa ne a taron babban zaɓen jam’iyyar na jiha, wanda ya kammala a safiyar Laraba ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu. Wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar sun amince da Doguwa da sauran ‘yan takarar maslaha ta hanyar kaɗa ƙuri’ar murya, a wani tsari da majiyoyin jam’iyyar suka bayyana a matsayin mai cike da zaman lafiya da gaskiya. Haka kuma, an ware kujerar shugabancin ga Yankin Sanatan…
Read More

Tinubu ya rantsar da Tunji Disu a matsayin Sufeto Janar na 23 a rundunar ‘yan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Laraba Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin sufeto janar na rundunar 'yan sandan Nijeriya (IGP) na 23. An gudanar da taron rantsarwar ne a sashen majalisa na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Hakan na zuwa ne gabanin zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), sannan ya samu halartar ministoci da wasu manyan jami'an gwamnati. An fara zaman na FEC ne jim-kaɗan da kamar taron rantsarwar. Waɗanda suka samu halarta sun haɗa da Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume; Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa,…
Read More