Babaji

5689 Posts

Ta tabbata Gwamnan Zamfara na yunƙurin sauya sheƙa zuwa APC, inji majiyar jam’iyyar

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata majiya mai ƙarfi daga jam'iyyar APC a Jihar Zamfara, ta tabbatar da yunƙurin canza shekar Gwamna Dauda Lawal daga jam'iyyarsa ta PDP zuwa APC nan ba da jimawa ba. Wani jigo a APC a Jihar da ya buƙaci Wakilin Jaridar Blueprint ya sakaye sunan sa, ya bayyana hakan a hirar da yayi da Wakilin mu ta Wayar tarho yau Asabar. A cewarsa, Gwamnan ya gabatar da kudurinsa na dawowa Jam'iyyar APC Mai mulki a Nigeria daga Jam'iyyar SA ta PDP kwanaki hudu da suka gabata Kafin wucewarsa Kasa Mai Tsarki don yin Umra. A…
Read More

An gano abin da ya hana Beckham zuwa fadar Trump tare da su Messi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yanayi na ƙoƙarin kafa tarihi, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami ta kai ziyara a Fadar Shugaban Amurka, wato White House domin murnar lashe gasar MLS Cup da ta yi a 2025. Saidai armashin ziyarar ya ragu a sakamakon rashin ganin ɗaya daga cikin tawagar ƙungiyar kuma sanannen tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa. Yayin da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi ta je Birnin Washington D.C., inda Shugaba Donald Trump ya karrama ta, David Beckham bai samu halarta ba saboda wani muhimmin al'amari da ya je yi a Nahiyar Yurop. Wasu daga cikin…
Read More

Abuja: ‘Yan bindiga sun sace ‘ya’yan fasto huɗu da matar ɗan bijilante da wasu 11

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane 16 ciki har da matar wani kwamandan 'yan bijilante da ƙanwarta da kuma 'ya'yan fasto guda huɗu ne aka yi garkuwa da su bayan wani hari da 'yan bindiga suka ƙaddamar a ƙauyen Peze da ke yankin Byazhi a Kubwa na Ƙaramar Hukumar Bwarin Birnin Tarayya Abuja. An ruwaito cewa 'yan bindigar sun je yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai tsakanin ƙarfe 9:30 da 10 na daren Talata, inda suka riƙa shiga gidajen jama'ar garin. Wani mazaunin yankin da ya gana da ShaharaReporters ya ce maharan sai da suka taru a…
Read More

DIG Frank Mba ya yi ritaya bayan shekaru 34 yayin da PSC ta tantance AIG bakwai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (DIG), Frank Mba tare da wasu manyan jami’an ‘yan sanda sun yi ritaya daga aiki a ranar Juma’a a ƙarƙashin hukumar yayin da ake sabunta shugabancinta. Frank Mba, wanda ya kasance DIG dake kula da horo da ci-gaban jami’an hukumar a hedikwatarta da ke Abuja, ya yi ritaya daga aikin gwamnati bayan shafe shekaru 34 yana aiki. Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda na ƙasar, Kayode Egbetokun, ya riga ya yi ritaya, yayin da sabon Inspector‑General of Police (IGP) Olatunji Rilwan Disu ya karɓi ragamar rundunar. Mba tare…
Read More

Tun a Nuwamba Isra’ila ta ke kitsa halaka Khamenei, inji Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaron Isra'ila, Isreal Katz, ya bayyana cewa tun a watan Nuwamba ƙasar ta ɗauki matakin halaka Shugaban Iran Ali Khamenei, inda ta shirya aiwatarwa bayan wata shida. Hare-haren Amurka da Isra'ila sun yi sanadiyyar mutuwar Khamenei ne a sa'o'in farko na yaƙin da ƙasashen ke yi da Iran, wanda aka fara a ranar Asabar ɗin makon da ya gabata. A yanzu yaƙin ya shiga mako na biyu ana gwabzawa wanda ya yi silar mutuwar jagororin ƙasar da kuma haddasa yaƙin shiyya inda Iran take kai farmaki a sassan Isra'ila, yankin Gulf da kuma…
Read More

An gurfanar ɗan Chana a Nasarawa kan ha’inci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, ta gurfanar da wani ɗan Chana mai suna Zhang Wen Hao a gaban Mai Shari'a Ibrahim Shekarau na Babbar Kotun da ke zaune a garin Mararabar Jihar Nasarawa. Ana tuhumar Zhang ne da laifi guda da ya shafi ha'inci, kamar yadda takardar ƙarar ta bayyana. A cewar ƙarar, Zhang a watan Maris na 2023 a yankin Suleja, ya yaudari wani mai suna Paul Yichol da N1,000 domin ya buɗe asusu a Bankin Access da sunansa da nufin amfani da shi…
Read More

Borno: Dakarun tsaro sun daƙile hare-haren Boko Haram a ƙananan hukumomi huɗu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na JTF da ke aiki a ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya sun yi nasarar daƙile yunƙurin ƙaddamar da wasu munanan hare-hare da 'yan ta'adda suka shirya a ƙananan hukumomin Konduga, Marte, Jakana da kuma Mainok da ke Jihar Borno. Mayaƙan 'yan ta'addar sun ƙaddamar da hare-haren da misalin ƙarfe 10:30 na daren Juma'a har zuwa ƙarfe 3:00 na asuba, inda suka gaza samun nasara sakamakon tsayin daka da dakarun tsaron suka yi, kamar yadda jami'in yaɗa labaran atisayen, Laftanal Kanal Sani Uba ya bayyana a wata…
Read More

Akwai yiwuwar Gwamnan Dauda na Zamfara ya koma APC saboda matsalolin PDP

‎Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, na duba yiwuwar sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki, yayin da wa’adin da Hukumar Zaɓe ta kasa (INEC) ta sanya ke ƙaratowa. Rahotanni sun nuna cewa, wasu manyan shugabannin APC a Abuja sun yi ƙoƙarin jawo hankalin gwamnan zuwa jam’iyyar, inda ake zargin sun yi masa tayin tikitin takarar gwamna kai tsaye a zaɓen shekarar 2027 idan ya koma APC.‎‎A cikin yarjejeniyar da ake zargin an tattauna, za a bai wa gwamnan kashi 40 cikin 100 na muƙaman siyasa da na zaɓe a jihar, yayin da sauran kashi 60 cikin 100…
Read More

Sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta yi iƙirarin hannu a kisan kiyashin Ngoshe, ta yi barazanar hari a Abuja da Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata ƙungiyar 'yan bindiga ta yi ikirarin ita ke da alhakin ƙaddamar da mummunan harin da ya auku a ƙauyen Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda sojoji da fararen da dama suka rasu tare da yin awon-gaba da mutane sama da 300 a harin na ranar Laraba. Maharan sun yi wannan ikirari me a wani faifan bidiyo da jaridar NewsPointNigeria ta samo, inda aka ga mutane biyar suna bayanin yadda aka ƙaddamar da harin da kuma shelanta nufinsu na karɓe iko da yankin. Da fari, an ruwaito cewa maharan sun…
Read More

An halaka mahaifin tsohon mataimakin gwamna a Ebonyi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindigar da suka yi awon-gaba da Sarkin ƙauyen Ndufu-Alike, Ezeogo Francis Igwe na Ƙaramar Hukumar Ikwo ta Jihar Ebonyi, sun halaka shi. Rahotanni sun bayyana cewa, Sarkin, wanda mahaifi ne ga tsohon mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe, an yi garkuwa da sh ien a ranar 1 ga watan Maris, 2026. Al'amarin ya faru ne a lokacin da 'yan bindigar suka kai farmaki akan babura a ƙauyen, inda suke yi garkuwa da shi tare da tafiya da shi zuwa wani wajen da ba sani ba. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Joshua Ukandu, ya bayyana…
Read More