Babaji

5689 Posts

Za a fara karatun digiri a Kwalejin Tarayya ta Bichi

Gwamnatin Tarayya ta sahale wa Kwalejin Ilimi ta Ƙasa reshen Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano yin kwasa-kwasan digiri domin kyautata ingancin ilimin al'umma a Nijeriya. Shugaban kwalejin, Dakta Bashir Sabo Abubakar ne ya bayyana haka a yayin tattaunawarsu da manema labarai a ofishinsa na FCE Technical da ke Bichi. Da yake jawabi, Dakta Bashir Sabo Abubakar, ya bayyana wannan cigaba da aka samu ta fuskar alakanta kwasa-kwasan da ake yi tsakanin jiya da yau a FCE Technical Bichi, wanda a halin yanzu ake koyar da sama da kwasa-kwasai ashirin (20) a cikinta. "A baya duk wani NCE program…
Read More

Gwamnatin Kano ta raba babura a Ƙaramar Hukumar Bichi

A ƙoƙarinta na cigaba da ayyukan jinƙai da kyautata rayuwar al'umma ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na, Gwamnatin Jihar Kano na cigaba da kai ziyara ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar waɗanda za su rabauta da baƙoncin gwamnan domin tattauna matsaloli da bijiro da hanyoyin magance su. A sanarwar da Jami'ar Yada Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, jim kadan bayan kaddamar da rabon babura guda hamsin (50) kyauta ga jama'ar yankin a sakatariyar ƙaramar hukumar. Shugaban karamar hukumar,…
Read More

Kwankwaso ya musanta goyon bayan zargin komawar Abba APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jagoran Jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya amince tare da bada goyon baya ga shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyya mai mulki, APC. Hakan na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin cewa Abba na shirin fita daga NNPP domin koma wa APC, lamarin da ya sa aka shiga fargaba acikin jam'iyyar da tunanin Kwankwaso ka iya sassauto adawarsa ta yawan sauye-sauyen sheƙar 'yan siyasa a Nijeriya. A daren Talata wayewar Laraba ne aka samu wasu rahotanni a kafafen sada zumunta da ke…
Read More

Nijeriya da UAE sun soke harajin kayayyaki 13,000 yayin yarjejeniya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na ƙarfafa alaƙar kasuwancin da ke tsakaninsu, Nijeriya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), sun soke harajin kayayyaki na sama da guda 13,000 don faɗaɗa damarmakin hada-hadar kayan Nijeriya. Gwamnatin Tarayya ta sanar da haka a ranar Talata inda ta ce ta soke dukkan harajin kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su Nijeriya daga UAE, yayin da ita ma ƙasar ta cire harajin na guda 7,315 na waɗanda shiga su daga Nijeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar Nigeria-UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement (CEPA). Ma'aikatar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba jari ta bayyana haka dalla-dalla…
Read More

Jami’ar UNIMAID ta wanke ɗaliban da aka zarga da alaƙa da Boko Haram

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'ar Maiduguri (UNIMAID) ta ƙaryata ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kama wasu daga cikin ɗalibanta akan zargin su da alaƙa da mayaƙan Boko Haram, tana mai bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al'umma. Rijistiran jami'ar, Ahmada Lawan ya bayyana haka a wata takarda da aike wa jaridar NewsPointNigeria sakamakon yawo da wani faifan bidiyo ke yi akan al'amarin, wanda ya tayar da hazo musamman a yankin Arewa maso Gabas. Ya ce, babu wani ɗalibin jami'ar da bincikensi ya nuna cewa yana da wata…
Read More

Ronaldo ya sake zura ƙwallo yayin da Al Nassr ta yi rashin nasara karo na uku a jere

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tauraron ɗan ƙwallon ƙafa, Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo ɗaya tilo a wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta sha kaye a hannun Al Hilal da ci 3 da 1, lamarin da ya jefa fatan lashe kofi na ƙungiyar a wannan kakar cikin mawuyacin hali. Da fari Ronaldo ne ya fara zura ƙwallo a wasan, wanda daga bisani ya cabe a lokacin da Al Nassr ta jan kati ta mai tsaron gidanta. Al Hilal ta yi nasarar ne ta 'yan wasanta Salem Al-Dawsari, Mohamed Kanno da kuma Ruben Neves. Wannan shi ne karo na…
Read More

Amurka ta aiko wa Nijeriya kayan yaƙi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa, Amurka ta kawo wa Nijeriya kayan yaƙi domin bunƙasa ayyukan hukumomin tsaro a sassan ƙasar. AFRICOM ta sanar da haka ta kafar X a yau Talata, inda ta ce tuni dakarun Amurka suka kai wa hukumomin Nijeriya kayan a Birnin Tarayya Abuja. Hakan wani ɓangare ne na tallafa wa ƙoƙarin Nijeriya wajen sauke ayyukanta na fannin tsaro da kuma ƙarfafa alaƙar tsaro da ke tsakanin ƙasashen biyu. Gwamnatin Tarayya ta ce, gwamnatin Amurka ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa haɗin-gwiwar tsaro da Nijeriya ciki har da samar da agajin ayyukan leƙen…
Read More

Manchester United ta naɗa Michael Carrick a matsayin kocin riƙo

A yau Talata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick a matsayin sabon manajan riƙo har zuwa ƙarshen kakar 2025/26. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da korar Rúben Amorim a makon da ya gabata, da kuma gajeren lokacin da Darren Fletcher ya yi. Ana ganin Carrick ya dawo tsohuwar ƙungiyar tasa ne don ceto ta daga halin da take ciki. Masu Taimaka Masa sun haɗa da Steve Holland, tsohon mataimakin kocin Ingila; Jonathan Woodgate, abokin aikin Carrick daga Middlesbrough; sai kuma Jonny Evans, wanda zai cigaba da taimaka wa fannin horarwa. A…
Read More

Katsina: An halaka biyu da raunata amarya yayin da ‘yan bindiga suka sace mahalarta aure

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari akan ayarin masu bikin aure a Unguwar Nagunda da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina, inda suka kashe mutune guda biyu. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma raunata wasu da dama ciki har da amarya. Al'amarin ya faru ne a daren Lahadi, inda 'yan bindigar suka buɗe wuta a yayin da ayarin bikin ke wucewa, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. Haka kuma, an sace wasu baƙi dai har yanzu ba a tantance adadinsu ba yayin farmakin. Wani jami’in…
Read More

Ribas: Har yanzu Fubara bai samu takardar tsigewa a hukumance daga Majalisar Dokoki ba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas bai samu takardar tsigewa a hukumance ba daga Majalisar Dokokin jihar kwana uku da 'ya'yanta 27 suka tada batun tsige shi da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu bisa zargin su da saɓa wa ƙa'idojin aiki. Bincike daga gidan gwamnatin da Fatakwal a daren jiya Litinin ya nuna cewa, babu wani saƙo a hukumance da aka aike wa gwamnan duk da alƙawarin hakan da Kakakin majalisar, Martin Amaewhule ya yi. Wani babban jami'in gidan da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin jagororin, wato…
Read More