Babaji

5689 Posts

CAF ta dakatar da Eto’o wasa huɗu da cin tarar sa kan rikici da alƙalin wasa a gaban shugabanta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta yi hukunci akan Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru (FECAFOOT), Samuel Eto'o akan nuna rashin ladabi yayin wasan kusa da na dab da na ƙarshe da ƙasarsa ta sha kaye a hannun Moroko a gasar kofin ƙasashen Afirka, AFCON. A sanarwar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Alhamis, kwamitin ladabtarwar CAF ya tabbatar da cewa an ɗauki matakin akan Eto'o ne sakamakon rashin biyayya da karya dokokin wasanni na Sashe na 2(3) na hukumar. A cewarta, an samu tsohon ɗan wasan…
Read More

Yadda Arbeloa ya fara kocin Madrid da ƙafar hagu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba ƙungiyar Real Madrid ta sake shiga mawuyacin hali sakamakon doke ta da Albacete da ke rukuni na biyu ta yi a gasar Copa del Rey da ci 3 da 2, wanda hakan ya haifar da rashin nasara a wasan farko na kociyanta Alvaro Arbeloa. Wasu na ganin hakan ya faru ne a sakamakon rashin wasu daga cikin zaƙaƙuran 'yan wasan ƙungiyar da suka haɗa da Kylian Mbappe, Jude Bellingham da Thibaut Courtois. Akan haka ne kocin ya zuba 'yan wasa Jorge Cestero da David Jimenez, wadsnya taɓa horar da su a…
Read More

AFCON 2025: Mawaƙi Davido ya magantu bayan asarar miliyan N71 sakamakon kayen Super Eagles

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya yi tsokaci game da ce-ce-ku-cen Soshiyal Mediya bayan ya rasa Dala 50,000, wato Naira miliyan 50 a sanadiyyar kayen da Super Eagles ta Nijeriya ta sha a hannun Moroko. A ranar Laraba Moroko ta doke Nijeriya da 4 da 2 a zangon bugun fenariti bayan shafe mintina 120 ana fafatawa a tsakanin ɓangarorin biyu. Gabanin wasan ne Davido ya sanya zunzurutun kuɗi har miliyan N71 a caca da nufin samun Naira miliyan 495 idan Super Eagles ta yi nasara. Saidai hakan bai…
Read More

Jami’ar Bayero ta yaba wa Hukumar Hadejia Jama’are kan kammala ayyukan samar da ruwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata ne tawagar Hukumar Gudanarwar Jami'ar Bayero da ke Kano ta kai ziyayar sada zumunta da godiya a Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are dan nuna jin daɗi da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwa a sassan jami'ar. Shugaban jami'ar, Farfesa Haruna Musa ne ya jagoranci tawagar zuwa ofishin hukumar domin bayyana jinjina da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwan bayan tsawon lokaci da jami'ar ta yi na fama da rashin wadataccen ruwa. Ya ce ayyukan da aka fara tsakanin watan Disamba a shekarar 2025 zuwa watan Janairu 2026 sun…
Read More

Ali Nuhu ya yi albishir ga Kannywood da Nollywood yayin cikarsa shekara biyu a NFC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar 12 ga watan Junairu, 2026 ne Babban Daraktan Hukumar Kula da Finafinan Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu ke cika shekaru biyu cif akan muƙamin. A yayin haka ne ya sanar da cewa, shekarar 2026 za ta samar da sabon salon ci-gaba ga masana'antun Nollywood da Kannywood da ke ayyukansu a Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare. A wani rubutu da Daraktan hulɗa da jama'a na NFC, Brian Etuk ya fitar, Dakta Ali Nuhu ya ce hakan zai taimaka wajen "inganta finafinansu, faɗaɗa hanyoyin rarrabawa a gida Nijeriya da wajenta, sauƙin samun tallafin kuɗi,…
Read More

Shugaban BUA ya ba ‘yan Super Eagles miliyan N700 duk da shan kaye a hannun Moroko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen Attajirin nan kuma Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabi'u, ya tabbatar da cewa zai bayar da kyautar Dala 500,000 ga tawagar 'yan Super Eagles duk da Nijeriya ta yi waje a gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025. A ranar Laraba, mai masauƙin baƙi, Moroko ta doke Nijeriya da ci 4 da 2 a zangon buga fenariti bayan an tashi babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu a wasan tsawon minti 120 da suka yi. Rashin nasarar zura ƙwallo a raga daga 'yan wasa Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi ne ya…
Read More

AFCON: Moroko za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Lahadi ne Moroko da ke jagorantar gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025 za ta fafata da takwararta ta Senegal a wasan ƙarshe. Hakan na zuwa ne bayan da ƙasar ta doke 'yan Super Eagles na Nijeriya da ci 4 da 2 a bugun fenariti a daren jiya Laraba yayin wasan dab da na ƙarshe. An ƙare wasan babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu a zangon mintina 90 da na ƙarin rarar lokaci, lamarin da ya kai su ga zangon fenariti. 'Yan wasan Super Eagles, wato Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi…
Read More

Yanzu-yanzu: Super Eagles sun yi adabo da AFCON bayan shan kaye a hannun Moroko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai masauƙin baƙi, wato Moroko ta tsallake rijiya da baya a yayin da ta doke Nijeriya da ci 4 da 2 a zangon bugun fenareti. Wannan al'amari ya ba ta damar kaiwa matakin wasan ƙarshe a Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025. An gudanar da wasan ne a Birnin Rabat, wanda ɗan wasa Youssef En-Nesyri ya yi bugun da ya bai wa Moroko nasar akan 'yan wasan na Super Eagles. Mai tsaron gida Yassine Bounou ya yi nasarar hana Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi zura ƙwallo a zangon. Wannan shi ne karo na…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ƙulla sabuwar yarjejeniya da ASUU don kawo ƙarshen rikicin shekaru 17

Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun rattaɓa hannu akan sabuwar yarjejeniya da nufin inganta harkokin karatun jami'o'i da tabbatar da ɗorewar al'amuransu. Rahotanni sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen sauya tsarin albashi da walwalar malaman jami’o’i, tare da kawo ƙarshen dukkan matsalolin aka jima ana fuskantar su har na tsawon shekaru 17. Yarjejeniyar ta kawo karuwar albashi da kashi 40 ga malaman jami’o’in tarayya da zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, tare da sabon tsarin biyan albashi da ya haɗa da CONUASS (Consolidated University Academic Staff Salary) da kuma CATA (Consolidated Academic Tools Allowance). Wadannan…
Read More

Gwamnatin Kano ta dakatar da likitoci kan barin almakashi a cikin majinyaciya har ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da asibitoci ta Jihar Kano ta ce ta tabbatar da rasuwar wata mahaifiyar 'ya'ya biyar mai suna Aishatu Umar, lamarin da ya auku sakamakon sakacin likitoci a asibitin da take jinya, wato Abubakar Imam Urology Centre a Kano. Haka kuma, ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiyar sun bar almakashi a cikin wata matar yayin da suke mata tiyata, al'amarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani. Wata sanarwa da ta fitar na cewa Babban Sakataren Hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya…
Read More