Babaji

5689 Posts

Jirgin Ƙatar Airways ya yi saukar gaggawa da fasinjoji 260 a Legas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a ne wani jirgin sama na Kamfanin Qatari Airways da ke ɗauke da fasinjoji 248 da ma'aikata 12 ya yi saukar gaggawa a Filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas jim-kaɗan bayan tashinsa. Al'amarin ya faru ne sakamakon lalacewa daga wani sashinsa. Majiyoyin filin jiragen sama sun shaida wa manema labarai a yau Asabar cewa matuƙin jirgin ya sanar da jami'an kula da hanyoyi (ATCs) matsalar jim-kaɗan da tashinsu, lamarin day a sa ya nemi saukar gaggawa kuma aka amince masa nan take. Da yake tabbatar faruwar al'amarin, Sakataren yaɗa…
Read More

Legas: Mahaifin ‘yan biyun da suka rasu a sanadin rigakafi na neman adalci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a Legas sun shiga halin cece-kuce bayan rasuwar wasu 'yan biyu masu kimamin watanni tara da haihuwa a ƙasa da sa'o'i 24 da yi musu allurar rigakafi a wani asibitin gwamnati (PHC) da ke Ƙaramar Hukumar Ojo a jihar. An ruwaito cewa, yaran masu sunaye Testimony da Timothy, an kai su Ajangbadi Primary Health Centre ne a safiyar ranar 24 ga watan Disamba, 2025 a inda suka rasu a washegari, wato safiyar Kirsimeti, lamarin da ya haddasa cece-kucen musamman akan neman a yi bincike tare da tabbatar da adalci akan waɗanda abin ya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta hana alƙalin alƙalai bin umarnin Majalisar Dokokin Ribas akan tsige Fubara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Ribas da ke zama a Fatakwal, ta haramta wa Alƙalin alƙalan jihar, Mai Shari'a Simeon Chibuzor Amadi, karɓa ko ɗaukar mataki akan kowane saƙon Majalisar Dokokin jihar da ya shafi batun yunƙurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu. Kotun na Ƙaramar Hukumar Oyibo da ke babban birnin jihar ce ta bayar da umarnin bayan gwamnan ya shigar da korafe-korafe guda biyu akan al'amarin. Akan haka ne kotun ta haramta wa Kakakin majalisar, Martin Amaewhule da wasu mutane 32 ciki har da Akawun majalisar da Alƙalin alƙalan cigaba da…
Read More

Atiku ya magantu kan komawar ɗansa APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin ɗansa, Abba Atiku Abubakar na koma wa jam’iyyar APC mai mulki mataki ne na raɗin kansa. A wani rubutu ta shafinsa na X, Atiku ya ce a tsarin dimukraɗiyya irin waɗannan lamuran ba sabon abu ba ne, ko da kuwa siyasa ta haɗu da alaƙar iyali. Ya ce, "A matsayina na ɗan dimukraɗiyya, ba na tilasta wa ’ya’yan na ra’ayi a kan abubuwa da suka shafi irin wannan lamarin haka kuma bazan tilasta wa ’yan Najeriya ba."…
Read More

Kashim Shettima ya tafi Guinea da Switzerland

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron rantsar da Shugaba Mamadi Doumbouya na ƙasar Guinea-Conakry. Haka kuma, Shettima zai halarci taron shekara-shekara karo na 56 na Harkokin Tattali na Duniya a Birnin Davos na Switzerland bayan rantsa da shugaban ƙasar Yammacin Afirkan. Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha a wata takarda da ya aike wa manema labarai, ya sanar da haka. Ya ce, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai wakilci Shugaba Tinubu a taron rantsarwar Shugaba Doumbouya a ranar Asabar, a Filin wasa na GLC…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka malamin addini a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka halaka wani malamin addini a yankin Layin Ɗan-Auta da ke Gundumar Kuyello a Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwarin Jihar Kaduna. Mazauna yankin sun aike wa jaridar Premium Time hoton gawar mamacin, da aka bayyana da suna Bello Abubakar, wanda na'ibin limami ne na wani masallacin ƙungiyar Izala da ke ƙauyen. An kai masa farmaki tare da kashe shi ne yayin da yake aikin jidar itatuwa a gundumar, wadda ke gabashin Birnin-Gwari. Wani mazaunin yankin da ya zanta da manema labarai, ya ce ana kai wa…
Read More

2027: Ɗan Atiku ya koma APC, ya bayyana goyon baya ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, wato Abba Abubakar, ya fice daga jam'iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki, yana mai bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar da haka a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda wasu jagororin APC daga yankin Arewa ta Gabas suka tarbe shi bisa girmamawa, ranar Alhamis. Da yake jawabi a taron, Abba ya sanar da yin murabus daga PDP da kuma shelanta…
Read More

Katsina: Mu na goyon bayan sulhun da zai kawo zaman lafiya – Ƙungiyoyin sa-kai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin tsaro na fararen hula masu goyon bayan sulhu a Jihar Katsina, Kwamared Shamsuddeen Salisu Na Alhaji ya bayyana haka a hira da manema labarai a ɗakin taro ta ƙungiyar 'yan jarida a Katsina. Ya ce, sun goyi bayan kokarin da gwamnatin jihar Katsina da al'ummar jihar sukayi,wajan shawo kan matsala tsaro ta amfani da hanyoyi. tattaunawa da yan bindiga.. Kwamared Na Alhaji ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matsaya ne bayan nazari da sukayi ta hanyoyi da dama da suka haɗa da tattaunawa da mutanen da ke zaune a kananan hukumomin da…
Read More

Oshoala ta nemi Nijeriya ta karɓi baƙuncin AFCON bayan zargin CAF da yi wa Moroko alfarma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tauraruwar Super Falcons ta Nijeriya, Asisat Oshoala, ta bayyana fushinta game da abin da ta kira da "bunƙasar mamayar Moroko da mu'amalanta ta musamman", lamarin da ya sa ta jefa ƙalubale ga shugabancin hukumar kula da lamuran ƙwallon ta Afirka (CAF), tana mai tirjewa akan Nijeriya ce ta fi cancanta ta karɓi baƙuncin gasar AFCON. Kalaman nata na zuwa ne jim-kaɗan bayan doke Super Eagles a wasan dab da na ƙarshe a gasar ta kofin ƙasashen Nahiyar Afirka da Moroko ta yi a ranar Laraba a zangon buga fenariti. Asisat, wadda gwarzuwar Afirka ce…
Read More

Jam’iyyar ADP ta jinjina wa sojoji bisa zagayowar Ranar ‘Yan Mazan Jiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar ADP ta miƙa saƙonta na gaisuwa da taya murna ga Rundunar Sojin Nijeriya a bisa zagayowar ranar tunawa da 'yan mazan jiya. ADP, wato 'Action Democratic Party', a wata takarda da ta fitar ta hannun Shugabanta, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ta tunatar da jarumta sadaukarwa da hidimta wa ƙasa ba tare da gajiyawa ba ga Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya da dakarun tsaron ke yi don al'umma da ma ƙasa baki ɗaya. Haka kuma, jam'iyyar ta bayyana karamcinta ga jami'am rundunar maza da mata da suka rasa rayukansu wajen kare haɗin kan ƙasa, iko da…
Read More