18
Jan
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta ƙaddamar da bincike akan zargin mummunan farmaki a gidan wani mai suna Haruna Bashir a Unguwar Ɗorayi Charanchi Quarters, wanda ya yi ajalin Fatima Abubakar mai shekarun 35 da 'ya'yanta shida. A cewar sanarwar da Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar, hukumar ta samu rahoton faruwar al'amarin da misalin ƙarfe 12:10 na ranar Asabar. Kiyawa ya bayyana cewa, an farmaki waɗanda abin ya shafa ne da wasu muggan makamai da wasu ɓata gari ke ɗauke da su ta hanyar kutse a cikin gidan. Ya…
