Babaji

5689 Posts

‘Yan sanda sun ƙaryata rahoton garkuwa da masu bauta sama da 100 a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Rabi'u, ya bayyana rahoton sace masu bauta sama da guda 100 a Ƙaramar Hukumar Kajuru a matsayin ƙarya da dillalan rikicin suka tsirar da nufin haddasa fitina a jihar. Wasu rahotanni a jiya Litinin sun yi ikirarin 'yan bindiga sun yi awon-gaba da sama da mutane 100 a lokacin da suke tsaka da addu'o'i a coci a Ƙauyen Kurmin Wali da ke Kajuru, ranar Lahadi. Da yake ganawa da manema labarai a yayin zaman majalisar tsaro ta jihar a ɗakin taro na Sir Kashim Ibrahim, ranar Litinin, Kwamishinan…
Read More

Jami’an DSS sun sake kama Malami jim kaɗan bayan sako shi daga kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matsalolin shari'a da siyasar tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) sun yi ƙamari yayin da a ranar Asabar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka sake yin ram da shi jim kaɗan bayan sako shi daga gidan yari na Kuje da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da Malami ofishin hukumar ne bayan cika sharuɗɗan belin da kotu ta ɗora masa a lokacin da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin sa da hannu a badaƙalar kuɗaɗe. A kwanakin baya ne…
Read More

Gwamnan Kano ya yi ganawar sirri da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin ne Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, lamarin da ke ƙara ƙarfafa jita-jitar sauya sheƙar gwamnan daga jam'iyyarsa ta NNPP zuwa APC mai mulki. Rahotannin sun nuna cewa Abba ya isa ofishin shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe 4:13 na yamma. Wannan ita ce ganawa ta musamman kuma ta farko da Shugaba Tinubu ya yi da wani tun bayan dawowarsa Nijeriya daga Abu Dhabi inda ya halarci taron harkokin ci-gaba na 2026. Duk da cewa ba a bayyana…
Read More

Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a Switzerland don halartar taron tattalin arziƙi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Nijeriya a taron Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) karo na 56 da za a gudanar a Birnin Davos na ƙasar Switzerland. Za a gudanar da taron ne daga yau 19 zuwa 23 ga watan Junairu, 2026 wanda wakilan ƙasashe da dama za su halarta. A cewar sanarwar da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya samu tarba daga Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole da jami'an jakadancin Nijeriya da ke ƙasar.‎‎A taron…
Read More

Yadda jami’ai suka cika hannu da dillalin ƙwayar da ya halaka jami’an NDLEA uku bayan shekara 12

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wani jagoran harkar dillancin ƙwaya da aka daɗe ana nema ruwa-a-jallo mai suna Lekan Jimoh da aka sani da "Kanmo-Kanmo". An yi nasarar haka ne bayan shekaru 12 da ake zargin sa da hannu a kisan wasu jami'an hukumar guda uku. A ranar Juma'a, 16 ga watan Junairu, 2026 aka kama Jimoh a garin Owode da ke Jihar Ogun bayan wani atisayen sirri da aka gudanar ƙarƙashin tawagar ayyukan na musamman ta hukumar. Haka kuma, a yayin bincike a maɓoyarsa, an gano kilogram…
Read More

‘Yan sanda sun kama uku bisa zargi da hannu a kisan uwa da ‘ya’ya shida a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane guda uku da zargi ya yi ƙarfi akansu na alaƙa da kisan matar aure da 'ya'yanta shida a Unguwar Ɗorayi Charanchi da ke jihar. An yi nasarar haka ne sakamakon wani atisayen sirri da jami'an hukumar suka gudanar a dare ranar 17 ga watan Junairu da safiyar washe-gari. A sanarwar da jami'in hulɗa da jama'arta, CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an yi nasarar haka ne a bisa umarnin Sufeto Janar na rundunar, Kayode Egbetokun da kuma kulawar Kwamishinanta na…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Senegal ta lashe AFCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tawagar 'yan ƙwallon ƙasar Senegal ta lashe kofin gasar ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025. Hakan ya biyo bayan doke Moroko da ce 1 da nema a zangon ƙarin lokaci bayan shafe mintina 90 da ɗoriya ba tare da ɗayansu ya zura ƙwallo a raga ba. Ɗan wasa Pape Gueye ne ya zura wata ƙayatacciyar ƙwallo a ragar Moroko, wanda hakan ya ƙayatar da masu kallo. Wannan shi ne karo na biyu da Senegal ta lashe gasar a tarihinta tun bayan samun na farko a 2021.
Read More

Shettima ya isa Guinea don halartar taron rantsar da Shugaba Doumbouya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya isa Conakry, Babban Birnin ƙasar Guinea domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu, a taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Mamady Doumbouya, Za a gudanar da taron ne ƙarshen mako, a filin wasa na GLC Stadium, Nongo. Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin Guinea da kuma mambobin ofishin jakadancin Nijeriya, gabanin bikin rantsarwar. Hakan ya nuna kawo ƙarshen wa’adin mulkin soja na tsawon shekaru huɗu bayan babban zaɓen da aka gudanar a watan Disambar 2025. Wakilcin da Mataimakin Shugaban Ƙasar ke yi ya jaddada rawar jagorancin…
Read More

Katsina: Sama da mutane miliyan uku sun halarci Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mabiya Ɗarikar Tijjaniya guda miliyan uku daga ciki da wajen Nijeriya ne suka taru a Katsina domin bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass na 2026 a ranar Asabar. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa an gudanar da taron ne a Filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Majma'u Ahbab Sheikh Ibrahim Nyass. Shugaban kwamitin shirya taron Sheikh Muhammad Hadi Balarabe ya ce sun samu aƙalla baƙi miliyan huɗu daga jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja da kuma ƙasashen Yamma da Arewacin Afirka. NAN ya ruwaito cewa, kusan dukkan ɗakunan…
Read More

Zamfara: APC ta musanta karɓar wasiƙar sauya sheƙa daga Gwamna Lawal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ke cewa ta karɓi wata takarda daga Gwamna Dauda Lawal na nema son shiga jam'iyyar. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa akwai zarge-zarge a jihar na cewa gwamnan na shirin komawa APC. A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Yusuf Idris ya fitar ranar Asabar a Gusau, ya bayyana zargin a matsayin abin da aka ƙirƙira da ba shi da asali ko tushe. A cewarsa, an ƙirƙiri zancen ne da nufin ruɗar da jama'a da ƙoƙarin haddasa rikici acikin jam'iyyar. Ya bayyana cewa,…
Read More