22
Jan
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da belin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu da wasu mutane uku da aka shigar da su ƙara tare akan Naira miliyan 100 ga kowannensu na zargin ɗaukar nauyin ta'addancin Dala miliyan 9.7. Haka kuma alƙalin ya umarci su Adamu da gabatar da mutane biyu-biyu da za su tsaya musu masu muƙaman babban sakatare ko darakta a aikin gwamnati. Sannan, ya umarci da a saki Yakubu har zuwa ranar 26 ga watan Fabarairu, 2026, inda za a cigaba da sauraron…
