Babaji

5689 Posts

Madrid ta naɗa sabon koci bayan sallamar Alonso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jim-kaɗan bayan raba gari da Xabi Alonso, ƙungiyar Real Madrid ta naɗa Alvaro Arbeloa a matsayin sabon mai horar da 'yan wasanta, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa. Arbeloa ya taɓa taka leda a Real Madrid a matsayinsa na ɗan wasan baya, inda ya samu manyan nasarori da kulob ɗin. Ɗan ƙasar Sifaniyar ya buga wasanni 238 wa Real Madrid daga shekarar 2009 zuwa 2016, inda ya lashe kofunan Champions League biyu da Laliga sau ɗaya da sauransu. Haka kuma da shi ƙasarsa ta lashe Kofin Duniya na 2010 Euro na 2008 da…
Read More

Real Madrid ta yi adabo da Alonso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Litinin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta raba gari da mai horar da 'yan wasanta, Xabi Alonso. Hakan na zuwa ne sa'o'i kaɗan da ƙungiyar ta sha kaye a hannun Barcelona a wasan ƙarshe na gasar Super Cup. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce sun amince su rabu da Alonso ne ta hanyar fahimtar juna domin a rabu lafiya. "Za mu cigaba da girmama Xabi Alonso a Real Madrid kuma yana da daraja da wuri na musamman." Ta ƙara da cewa, tana godiya da gudunmuwar da ya bayar…
Read More

Jami’an tsaro sun yi cincirindo a gidan gwamnatin Kano gabanin tsammanin sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC

Rundunonin jami’an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen harabar Gidan Gwamnatin Jihar Kano a jiya Litinin, sakamakon rahotannin da ke yawo kan yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa Jam’iyyar APC. Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun hallara domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana duk wani abu da ka iya tayar da hankalin jama’a.‎An ruwaito cewa jami’an tsaron da aka jibge sun haɗa da ’Yan Sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya DSS, inda aka kafa su a babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin da sauran muhimman wurare. Haka kuma, an ga aƙalla motoci…
Read More

An ceto yara 25 da aka sace a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da ceto yara guda 25 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Wase daga hannun 'yan bindigar da suka yi basaja a matsayin 'yan bijilante. Rahotanni sun bayyana cewa tun a ranar 21 ga watan Disambar 2025 ne aka sace yaran a hanyar Zak zuwa Sabon Layi da misalin ƙarfe 7 na yamma a lokacin da suke kan hanyar tafiya zuwa wajen bikin Mauldi. Uku daga cikinsu sun yi nasarar tserewa yayin faruwar al'amarin, kamar yadda rahotanni suka shaida. Da yake ganawa da manema labarai a ranar…
Read More

Siyasar Kano na rawa yayin da Gwamna Abba ke shirin koma wa APC a yau

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin ne ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano zai sauya sheƙa daga Jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki, lamarin da ke nuna samuwar muhimmin sauyi a siyasar jihar tun bayan zaɓen 2023. Wani mamban kwamitin zartarwar jihar ya tabbatar da haka ga manema labarai a safiyar Litinin, inda ya ce tuni gwamnan ya kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki a jihar ge da shirin sauya sheƙar. Ya ce: " Eh, lallai gwamnan zai koma APC a yau Litinin tare da dukkan magoya bayansa", inji kwamishinan, wanda bai…
Read More

Borno: ‘Yan ta’addar da suka sace ciyaman sun nemi a biya fansar Dala 300,000

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ciyaman na Ƙaramar Hukumar Biu da ke Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, Hassan Biu Miringa, ya yi magiya daga komar waɗanda suka yi garkuwa da su, inda ya ce masu garkuwar na neman a biya fansar Dala 300,000 domin sako shi da tare da wani mutum guda da aka tsare. Rahotanni sun bayyana cewa, Miringa, wanda shi ne ciyaman na ƙaramar hukumar a tsakanin shekarun 2020 da 2022, an sace shi ne tare da wasu kansiloli biyu na gundumomin Zarawuyaku da Miringa a watan Disambar 2025. Al'amarin ya faru ne akan…
Read More

Ganduje ya shirya tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan siyasar Kano bayan dawowarsa Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo gida Nijeriya bayan shafe makonni yana hutu a Dubai ta ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). Haka kuma ya shirya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasa musamman waɗanda suka shafi ci-gaba a Jihar Kano. A wata takarda da Shugaban ma'aikatansa Muhammad Garba ya fitar, Ganduje ya ce ya shirya tattaunawa da ɓangarorin daban-daban da nufin ƙarfafa haɗin kai acikin jam'iyya yayin da alƙiblar siyasar jihar ke ɗaukar wani salo. Sanarwar ta kuma ƙunshi cewa Ganduje zai…
Read More

AFCON 2025: Shugaban BUA ya yi alƙawarin Dala 500,000 ga ‘yan Super Eagles matuƙar suka kai wasan ƙarshe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hamshaƙin ɗan kasuwa kuam Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabi'u, ya taya 'yan wasan Super Eagles murnar nasarar da suka samu a ranar Asabar a gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON), inda suka doke tawagar Algeria da ci 2 da 0. A wani rubutu a shafinsa na sada zumunta, attajirin ya bayyana farin cikinsa da kuma alfaharin da ya ke da shi kan kungiyar ta kasa, inda ya ce nasarar ta kara wa 'yan Najeriya kwarin gwiwa yayin da suke shirin fuskantar wasan rabi na karshe wato Semi-Final. Shugaban na BUA ya kuma yi…
Read More

Gobara ta lanƙwame gidan ruwa a Ƙaramar Hukumar Bichi

Gobara ta afku a gidan ruwan tsohon ɗan majalisa, marigayi Ibrahim Mu’azzam da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano sakamakon tartsatsin wutar lantarki. Ɗan marigayin, Nura Ibrahim Mu'azzam wanda ya bayyana haka, ya ce gobarar ta yi sanadiyar asarar abubuwa da dama a gidan ruwan. Sanarwar dai ta Nura Ibrahim Mu'azzam, ta bayyana cewa wannan gobara ta jefa iyalai da maƙwabta da dama a cikin tsananin firgici. Amma, duk da haka, mazauna yankin sun yi gaggawar kai dauki domin hana wutar yaduwa zuwa wasu gidaje. Hukumar kashe gobara ta Bichi ta yi nasarar daƙile wutar kafin ta ƙara yaɗuwa…
Read More

Kano: An kwaɗaitar da al’umma rajistar katin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Bichi

An bbuƙaci al'umma a Ƙaramar Hukumar Bichi da su cigaba da fitowa wajen tabbatar da mallakar katin zaɓe ga wanda bai da shi ko yake da matsala domin samun damar kaɗa kuri'arsa a zaɓe mai zuwa na 2027. A sanarwar da Jami'ar Yada Labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, wannan kira ya biyo bayan zaman tattaunawar masu ruwa da tsakin yankin ne a kan tabbatar da adalci ga jama'ar karamar hukumar dangane da zabe mai gabatowa, a ofishin gudanar da al'amuran zabe na yankin. Kwamitin masu ruwa da tsakin sun cimma fahimtar tantance ababen da…
Read More