Babaji

5702 Posts

An miƙa jaddawalin sabbin jihohi 46 da ake neman kafawa a Nijeriya ga Majalisar Wakilai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin gyare-gyaren kundin dokokin 1999 na Majalisar Wakilai ya ce, ya karɓi takardun buƙatun kafa sababbin jihohi guda 46 a Nijeriya tare da ƙananan hukumomi 117. An samu takardun ne daga ƙungiyoyin da ke da muradin samar da jihohin daga shiyyoyi guda shida na faɗin ƙasar. Ga jaddawalin buƙatun kafa jihohin kamar yadda News Point Nigeria ta ruwaito: "North East Savannah State – from Borno Kwararafa State – from Taraba Katagum State – from Bauchi Amana State – from Adamawa South Sardauna State – from Taraba Muri State – from Taraba North West 7.…
Read More

Atiku, Obi, ministocin Buhari da tsofaffin shugabannin APC sun karɓi jam’iyyar ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da ake cigaba da shirin tunkarar babban zaɓen 2027, haɗakar ƴan siyasar adawa ta karɓi jagorancin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, ranar Laraba. A taron, an ga wasu daga cikin ministocin da suka yi aiki da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da mambobin kwamitin ayyuka na APC. Haka kuma, an gudanar da taron ne a ɗakin taro na Yar'Adua Centre dake birnin Tarayya Abuja, inda Shugaban jam'iyyar, Cif Ralph Nwosu ya ce ADC ta gudanar da zaman kwamitin zartarwa (NEC) guda 12 a cikin watanni 18. Ya ce, Nijeriya ta…
Read More

KANNYWOOD: Abba Al-Mustapha ya fara kama ƴan Kwankwasiyya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Abba Almustapha, ya yi wani wawan kamu a jihar, inda ya kama ɗaya daga cikin zaratan siyasar Kwankwasiyya a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood mai suna Umar UK. An kafa wannan tarihi ga siyasar Kwankwasiyya ne a jiya Laraba, 2 ga Yuli, 2025, bisa zargin da hukumar ta ke yi wa UK na fitar da shiri mai dogon zango mai suna Garwashi ba bisa ƙa'ida ba, wanda suka ɗauki nauyi tare da Mai Taimaka Wa Gwamna ta Musamman, Fauziyya D. Sulaiman. Jami’an Hukumar Sibil Difens ne suka…
Read More

Jikin Buhari ya yi tsanani yayin da aka ba shi gado a Asibitin Landan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An kwantar da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a ɗaki na musamman (ICU) wani asibiti a Landan saboda fama da matsananciyar rashin lafiya. Jaridar 'TheCable' ta rawaito daga 'Empowered Newswire' cewa, wani makusancin tsohon shugaban ya ce Buhari ya kamu da rashin lafiyar ne a Landan a yayin da ya je domin a duba lafiyarsa. Rahoton ya ce, an kwantar da Buhari a ɗakin ICU, amma daga bisani aka sallame shi makon da ya gabata. Kodayake ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, amma rahotanni sun nuna cewa yana samun sauƙi a…
Read More

MOPPAN ta yi tir da kalaman Al-Hikima na sukar ƴan Kannywood

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta yi alla-wadai da kalamai marasa daɗi da wani Abdullahi Al-Hikima da ke sayer da maganin gargajiya ya yi akan ƴan masana'antar fina-finai ta Kannywood. A sanarwar ta Babban Sakataren ƙungiyar, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel ya fitar, MOPPAN ta ce lallai mai maganin ya ci zarafinsu duk da cewa su ne silar shahararsa a duniya. Ta kuma bayyana shi a matsayin mara kunya, mutunci da yakana gami da saurin manta alheri da masana'antar ta yi masa. Akan hakan ne ƙungiyar ta yi jinjina ga waɗanda suka bayyana…
Read More

An naɗa David Mark da Aregbesola a matsayin shugaba da shakaren riƙon ƙwarya a ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani yunƙuri na samar da tafiyar da za ta kawo ƙarshen mulkin Shugaba Bola Tinubu a 2027, ƴan ɓangaren adawa a jam'iyyar ADC, sun naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare na riƙon ƙwarya a jam'iyyar. Muryoyi da dama bayan kammala zaman ƴan jam'iyyar a daren ranar Talata wayewar Laraba sun shaida cewa, jagorancin jam'iyyar ya amince da naɗin mutane biyun. Haka kuma, muryoyin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu kasancewar ba a ba su izinin bayyana hakan ba a hukumance,…
Read More

Kashim ya wakilci Tinubu wajen sake buɗe sabon titi a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Talata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilta, ya sake ƙaddamar da sabon titi a birnin tarayya Abuja. Aikin titin, wanda ya taso tun daga Obafemi Awolowo Way a Jabi ya haɗa da sauran hanyoyin gundumar ɗaki biyu. Kazalika, sabuwar hanyar ta haɗa hedikwatar hukumar ‘yan sanda da babbar kotun tarayya da ke Jabi da hedikwatar kotun ɗa’ar ma’aikata, da sabon sashin Kotun Ɗaukaka Ƙara na Abuja. Aikin titin da gwamnatin babban birnin tarayya ta aiwatar na daga cikin ƙoƙarin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi…
Read More

Ɗangote ya sake rage farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matatar mai ta Ɗangote ta sake rage farashin litar fetur ga masu dako daga gare ta daga N880 zuwa N840. Babban jami'in hulɗa da jama'a na rukunin kamfanin Ɗangote, Anthony Chiejina wata sanarwa ya tabbatar da haka a ranar Litinin. Ya ce, ragin ya fara aiki ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2025. Hakan wani mataki ne na sauƙaƙe wa al'umma da kuma la'akari da sauye-sauyen farashi da ake samu a kasuwannin cinikayyar ɗanyen mai.
Read More

Asibitin ƙwararru na Best Choice ya rage kaso 50 na kuɗaɗen ayyuka da buɗe fayil kyauta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 50 na kuɗaɗen ayyukansu na yau da kullum, wanda suka haɗa da kudin ganin likita kudin Gado da sauran ayyukan su, shi kuma bude Fayal ya zama kyauta ne yanzu haka. Hakan na kunshe ne Cikin wata tattaunawa da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal yayi da Jaridar Alfijir Labarai a yau Talata. Lawal yace bayan korafe-korafe da kiraye-kirayen da jama a suke ta yiwa asibitin hukumar gudanarwar sun yi kwakkwaran bincike har suka gano yadda wasu suke kasa zama har lokacin da ya dace likita…
Read More