Babaji

5702 Posts

Harin jirgin ƙasa: Kotu za ta saurari buƙatar belin Tukur Mamu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta shirya sauraron sabuwar buƙatar da Tukur Mamu ya shigar, wanda ake zargin sa da zama wakilin tattaunawa na ƴan ta'adda a lokacin da suka farmaki matafiya a jirgin ƙasa akan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja a watan Maris, 2022. Alƙali Mohammed Umar a yayin zama a kotun ranar Litinin, ya ce za saurari buƙatar belin nasa ne a ranar 22 ga watan Yuli. Lauya mai kare Mamu Johnson Usman (SAN) ya nemi a ɗage batun a ranar Litinin domin ya samu damar yin nazari game da takardar…
Read More

Zamfara: An kashe ƴan ta’adda da dama har da ɗan uwa ga Turji

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yayin wani ba-takashi da aka yi a tsakanin dakarun tsaro da ƴan bindiga ne aka yi nasarar halaka Yello Ɗan-Bokolo, wanda ɗan uwa ne ga Bello Turji. An kuma kashe wasu ƴan bindiga da dama a yayin gumurzun, wanda aka yi a Ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara. Ɗan-Bokolo, wanda rahotanni sum bayyana cewa ya fi Turji rashin tausayi, ya rasa ransa ne a sakamakon raunukam da ya samu a ƙarshen mako, wanda aka yi jana'izarsa a ranar Asabar da ta gabata. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, mazauna sun ce aƙalla ƴan…
Read More

Kasafin Ribas: Majalisar Wakilai ta gayyaci kantoman Ribas kan ware biliyan N24 ga CCTV na gidan gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙwarya-ƙwaryan Kwamitin Majalisar Wakilai akan Ribas, ya bada kwana biyu ga Kantoman jihar, Ibok-Eke Ibas na ya miƙa masa rahoton dalla-dalla akan manyan ababen da aka sanya a kasafin tiriliyan 1.48 na jihar. Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere (APC Edo) ya sanar da hakan ne a yayin zaman kare kasafin a Abuja. Ya ce, kwamitin ya yi nazari akan kasafin, wanda kantoman ya gabatar, inda aka samu bututuwa da dama da suke buƙatar ƙarin bayani. Ihonvbere, ya umarci kantoman da ya gabatar da takardar rahoton kashe-kashe na tsakiya zango. Ɗan majalisar, wanda shi ne shugaban…
Read More

Dokar ta-ɓaci: Ta yiwu Tinubu ya dawo da Fubara da ƴan majalisa shugabancin Ribas a Yuli

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun nuna cewa, Shugaba Bola Tinubu yana shirin dawo da dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da tawagar ƴan Majalisar Dokokin jihar a wannan watan na Yuli. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya jaogranci sulhunta tsakanin gwamnan da Ministan Abuja Nyesom Wike, bisa rikicinsu na tsawon lokaci. A watan Maris ne aka tsayar da rikicin siyasar jihar a yayin da Shugaba Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar na tsawon watanni shida, inda ya kafa hujja da matsalolin tsaro da ya shafi…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Fusatattun matasa sun ƙone ofishin NDLEA da lalata fadar sarki a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin newasu fusatattun matasa a garin Lafiagi dake Ƙaramar Hukumar Edu ta Jihar Kwara suak karaɗe tituna, inda suka gudanar da zanga-zanga kan ƙamari da rashin tsaro ya yi a yankunansu, lamarin da ya haɗa da ta'addanci, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe. A wani faifan bidiyo an ga yadda suke ɗaga allunan ɗauke saƙonnin da ke nuna suan da buƙatar ɗauki na gaggawa kan zubar da jini da ake yi da garkuwa da mutane da ya zama ruwan dare a yankunan. Blueprint ta ruwaito cewa, matasan Irate sun banka wa ofishin…
Read More

An ɗage jana’izar Ɗantata zuwa ranar Talata – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu a ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya shaida wa BBC batun, idna ya ce hakan ya samu ne a sakamakon rashin isar gawar marigayin akan lokaci zuwa birnin Madina. ''Akwai ƙa'idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana'iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,''in ji ministan. Ya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta ayyana 24 ga Yuli a matsayin ranar zaman NEC don maye gurbin Ganduje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yayin zaman Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na APC ne aka zaɓi 24 ga watan Yuli a matsayin ranar da za gudanar da zaman Majalisar Zartarwar (NEC) jam'iyyar domin naɗa sabon shugaban jam'iyya. A ranar Juma'a ne Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar, lamarin da ya sa mataimakinsa na Arewa, Bukar Dalori ya karɓi kujerar na riƙon ƙwarya. Bayan taron gaggawa na NWC'n ne a yayin ganawa da manema labarai, Mataimakin Sakataren jam'iyyar, Barista Festus Fuanter ya ce zaman zai bada damar naɗa sabon shugaba. Ya kuma ce, tuni aka…
Read More

Zaman NEC: ‘Yan sanda sun karɓe iko a Sakatariyar PDP da umartar mambobin Kwamitin Amitattu su bar farfajiyarta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar ranar Litinin ne jami'an ƴan sanda suka karɓe iko da Wadata Plaza, wato Hedikwatar babbar jam'iyyar adawa (PDP) dake Abuja, a sakamakon fargabar rikicin zaman Kwamitin Majalisar Zartarwar jam'iyyar (NEC), wanda ake sa ran gudanarwa a yau. Ƴan sandan sun hana mambobin kwamitin amitattun (BoT) jam'iyyar ciki har da Maina Chiroma shiga farfajiyar Sakatariyar. Tsohon Sakataren jam'iyyar, Umar Tsauri ya shaida wa manema labarai cewa, ƴan sanda sun kafa musu hujja da cewa an ba su umarnin hana mambobin Bot shiga ne daga mataki na sama. Daga bisani an ga yadda mambobin…
Read More

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta isa Saudiyya don binne Ɗantata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya ta sauka a Saudiyya domin karɓar gawar hamshaƙin Attajiri kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasa, marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, yayin da ake shirye-shiryen yi masa jana'iza a Madinah. A safiyar ranar Asabar ne Ɗantata, wanda ya shafe shekaru 94 a duniya ya rasu a Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). A sanarwar da mai taimaka wa Ministan Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Rabi'u Ibrahim ya fitar ranar Litinin, ya ce tawagar, wadda ta bar Nijeriya a yammacin ranar Lahadi, ta isa Madinah a safiyar yau Litinin. Ministan…
Read More

APC ta bayyana matsayar Tinubu akan murabus ɗin Ganduje da batun sauya sheƙar Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa tana gudanar da shawarwari game da batun maye gurbin tsohon shugabanta, Abdullahi Ganduje, wanda ya yi murabus a makon da ya gabata. Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Felix Morka a wata hira da gidan telebijin na 'Channels', ya ce APC tana aiki da lissafi wajen ganin ta cike gurbin da ganduje ya bari. Ya kuma ce, za a sanar da sabon shugaban jam'iyyar ne a yayin gudanar da babban zamanta na ƙasa, wanda kawo yanzu ba a bayyana ranar da za a yi haka ba. Game da batun yiwuwar…
Read More