30
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen samun tsawa da yanayi na ruwan sama daga ranar Litinin zuwa Laraba a faɗin ƙasar. A saƙon hasashen yanayin da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, NiMET ta ce akwai yiwuwar samun hadari ma ɗauke da tsawa a sa'o'in safiya a Jihohin Sakkwato Kebbi, Zamfara, Taraba, Adamawa da Kaduna a Arewacin Nijeriya, a yayin da kuma za a yi rana a sauran sassan shiyyar. Ta kuma ce, ana tsammanin samun ruwan sama da tsawa a lokutan rana da dare a yankunan Jihohin Adamawa,…
