Babaji

5702 Posts

An sake zaɓar Eze Anaba na Vanguard a matsayin shugaban Ƙungiyar Editoci ta Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Editan jaridar Vanguard, Charles Eze Anaba ya sake zama shugaban Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a wani karon bayan sake zaɓar sa da aka yi a babban taron ƙungiyar da aka gudanar da ɗakin taro na ƙasa dake Enugu. Anaba ya sake tale kujerar shugabancin ƙungiyar ne bayan sake naɗa shi da aka yi ba tare da abokin karawa ba, lamarin da ake ganin ya faru ne saboda ƙoƙarinsa a jaograncin muƙamin. Haka kuma an zaɓi Onuoha Ukoh na jaridar The Sun a matsayin Babban Sakatare da ƙuri'u 218 sakamakon doke Wole Sogunle da…
Read More

Za a warware matsalolin sauyin yanayi ne ta ɗaukar matakai a aikace, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin sauyin yanayi. Shettima ya bayyana hakan a matsayin hatsarin da ya zama wajibi a yi ƙoƙarin kauce masa a aikace. A cewars, hakan ba abu ne da za a yi shi a ɗakin taro ba, saida yana buƙatar kowace ƙasa ta ɗauki matakin magance nata bisa la'akari da matsalolin da ta ke fuskanta a fannin. Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin ƙaddamar da shirin inganta muhalli na 'Green Legacy Initiative'…
Read More

Tinubu ya yi jimamin rasuwar Aminu Ɗantata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyarsa ta rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, attajirin ɗankasuwa da ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a safiyar yau Asabar. Ɗantata ya rasu ne bayan shafe shekaru 94 a duniya. Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗankasuwar, wanda aka binne a Saudiyya a matsayin rashi ga Nijeriya baki ɗaya'. Ya kuma yaba da gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen ciyar da gaba gaba musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya. A sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce, "mun yi rashi…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta kori ƴan Chana 14 bisa taimaka wa ta’addanci a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a wata Babbar Kotu a Jihar Lagas ta yanke hukunci ga wasu ƴan Chana guda 14 kan samun su da laifin kitsa ta'addanci ta yanar gizo da damfara a intanet. Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta ce mutanen suna daga cikin waɗanda aka kama da manyan laifuka ta intanet a Legas bayan gudanar da wani atisaye a ranar 19 ga watan Disambar 2024. A sanarwar da EFCC ta fitar ta kafar X, ta ce ƴan Chanan suna cikin mutane 792 da aka kama da hannu a damfara ta…
Read More

APC ta naɗa Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa a Arewa, Alhaji Bukar Dalori ya zama sabon Shugaban jam'iyyar na riƙon ƙwarya biyo bayan yin murabus da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi a ranar Juma'a. Sashe na 14(2) na kumdin dokokin APC ya bai wa mataimakin shugaban jam'iyyar na Ƙasa damar taimaka wa shugaban jam’iyyar wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa. Zuwa lokacin fitar rahoton, ba a samu cikakken bayanin da ya sa Ganduje yin murabus ba, lamarin da ya jefa ma'aikatan ofishin da masu ziyara cikin ruɗani. An ruwaito cewa, tsohon gwamnan na…
Read More

Hamshaƙin Attajiri, Aminu Ɗantata ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shahararren babban ɗan kasuwa daga Jihar Kano kuma mai taimaka wa al'umma, Alhaji Amina Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 a duniya. Wata majiya daga iyalan mamacin ta shaida wa jaridar 'News Point Nigeria' batun, inda ta ce ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Abu Dhabi a daren ranar Juma'a wayewar Asabar. Marigayin ya rasu ne da misalin karfe 3 na dare agogon Nijeriya. Ta kuma ce, an fara shirye-shiryen kawo gawarsa Nijeriya domin yin mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Sanannen attajirin, ɗaya ne daga cikin ƴan kasuwar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni daga gidajen jaridu sun bayyana cewa, Shugaban Jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa, lamarin da tuni ya fara aiki nan take. Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya ce ya ɗauki matakin ne saboda dalilai masu alaƙa da kiwon lafiyarsa, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda shi ne daidai a gare shi. Hakan na zuwa ne a lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa jam'iyyar na shirin gudanar da sauye-sauye. Kawo yanzu babu wani mai muƙami daga cikin APC da ya yi tsokaci game da wanda…
Read More

Ribas: An kai ƙarshen rikicin siyasar Wike da Fubara bayan Tinubu ya gana da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara, Ministan Abuja Nyesom Wike, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Ribas da mambobin majalisar. An yi zaman ne da nufin sulhunta tsakanin ƴan siyasar, wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta bisa rikicinsu da ya yi sanadin sanya dokar ta-ɓaci a jihar a ranar 18 ga watan Maris. Shugaba Tinubu ya yi hukuncin dakatar da gwamnan da ƴan majalisar ne saboda rashin neman hanyoyoyin aiki tare duk da rikicin da ke tsakaninsu da kuma halin tsaro a jihar da suaran su. Hotunan da aka…
Read More

Kotu a Nasarawa ta yanke wa wanda ya kashe ƴar hidimar ƙasa hukuncin rataya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Jihar Nasarawa dake Lafiya ta yanke wa wani Oluwatimileyin Ajayi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe budurwarsa mai suna Salome Adaidu. Rahotanni sum bayyana cewa, mai laifin ya kashe Salome ne, wadda ƴar hidimar ƙasa ce ta NYSC, da kuma yi wa gangar jikinta gunduwa-gunduwa. A yayin hukunci game da lamarin, Alƙali Simeon Aboki ya ce an samu Ajayi da laifin kashe ƴar hidimar ƙasar da kuma daddatsa sassan jikinta, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataye shi. A lokacin da ya…
Read More

Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin dokar Hukumar NDLEA

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya yi watsi da ƙudirin dokar yin kwaskwarima ga dokar Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta 2025. Ƙudirin dokar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito, na neman a bai wa hukumar ikon mallake wani yanki daga cikin kuɗaɗen da ta tatso a yayin kama waɗanda aka samu da aikata manyan laifukan da suka shafin ƙwaya. A ranar Alhamis ne a yayin gudanar da zaman Majalisar Wakilai, Kakakinta Tajudeen Abbas ya karanta ƙudirin. Saidai, a lokacin da ya ke tsokaci game da batun, Shugaba Tinubu, wanda…
Read More