26
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen birnin tarayya Abuja ta ce tana shirin shiga yajin aiki a yayin da Shugaba Bola Tinubu ya kammala ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a ranar 3 ga watan Yuli. Shugabanta, Dakta Stephen Knabayi ya bayyana hakan a yayin hira da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abuja, ranar Alhamis. Ya ce, za su tsunduma yajin aikin ne domin ankarar da hukumar gudanarwar birnin ta magance matsalolin da ke sa ma'aikata nazarin shiga yajin aiki. NAN ya ruwaito cewa, an rufe ƙananan asibitoci, sannan malaman makaratun firamare suna zaune a…
